
A jiyane kasar Congo ta doke Najeriya da ci 4-3 a bugun daga kai sai me tsaron gida(Penalty) bayan wasan su ya kare da 1-1.
Hakan ya hana Najeriya zuwa gasar cin kofin kwallon Duniya da za’a yi a shekarar 2026.
Bayan kammala wasan, Kocin Najeriya, Éric Chelle yace kasar Congo sun rika yin sihiri ne da ruwa.