
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyanawa ma’aikatun wutar Lantarki na kasa cewa Gwamnati ba zata sake amincewa da rashin samar da wutar lantarkin ba.
Ya bayyana hakane bayan amincewa da sabon daftarin gyaran wutar.
Yace kuma an samar da wani sabon tsari na baiwa ma’aikatan wutar Lantarkin horaswa ta musamman. Inda yace nan da shekaru 10 za’a magance matsalar karancin ma’aikata a hukumar wutar lantarkin.