
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya soke karin kaso 5 akan kamfanonin Sadarwa da ake shirin yi.
Shugaban hukumar NCC, Aminu Maida ne ya bayyana hakan a yayin zantawa da manema labarai.
Yace karin harajin kaso 5 akan kamfanonin sadarwar yana kunshene a cikin sabon kudirin dokar da majalisa ta amince dashi.
Yace yana wajan aka kawowa shugaba Tinubu maganar karin amma yace ba zai kara saka ‘yan Najeriya a cikin matsala ba.
Yace a baya an dakatar da karinne amma yanzu an cireshi gaba daya.