Thursday, May 14
Shadow

Babbar Kotun jihar Kaduna ta sake daga sauraron bayar da belin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sai zuwa watan June

Da alama dai Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ba zai samu damar halartar zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC ba.

Saboda Mai shari’a Darius Khobo na babbar kotun jihar Kaduna ya sake daga sauraron belinsa sai satin farko na wajan Yuni.

ICPC na ci gaba da tsare malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda ake zarginsa da almundahanar kudade da aikata ba daidai ba da mukamin da ya samu na Gwamna da sauransu.

Jam’iyyar ADC dai ta tsayar da karshen watan Afrilu zuwa Mayu dan gudanar da zaben fidda gwani.

Karanta Wannan  NNPC Ta Sanar Da Kammala Biyan Bashin Dala Bilyan 2.4, Tare Da Albishirin Samar Da Manyan Tashoshin CNG 12 A Shekara Mai Zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *