Thursday, January 2
Shadow

BABU INDA DANGIN MIJI SUKA TAƁA SAKIN MATA DAN HAKA AMINU ADO YA DAWO KUJERARSA, CEWAR RASHEEDA MAISA’A

Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, kuma tsohuwar mai baiwa Ganduje shawara, Rasheeda Adamu Abdullahi Maisa’a ta bayyana cewa har yau Aminu Ado Bayero shi ne halastaccen sarkin Kano kuma ya dawo kujerarsa domin babu inda dangin miji suka taɓa sakin mata saboda ba su ne suka aura masa ita ba.

Jaridar Dokin Karfe TV ta jiyo tsohuwar hadimar ta Ganduje wato Rasheeda Adamu Abdullahi Maisa’a na cewa yanzu haka Aminu yana Nasarawa kuma za su ɗau wanka su fita Ido yana gani su raka shi fadarsa batare da zare Ido ba. “Sarki Aminu mutum ne mai tsoron Allah har zuci ba a baki ba. Kuma ba a taɓa sarki mai haƙurinsa ba, ba ya tsoma baki da katsalandan cikin siyasa”.

Mai Sa’a ta kuma ƙara da cewa Sarki Aminu bai zo Kano don ya tada tarzoma ba, domin ya san muhimmancin zaman lafiya. “Muna kira ga shugaban ƙasa da mataimakinsa da su kawo wa Jihar Kano ɗauki ka da su bari wasu su hargutsa zaman lafiyarta”. In ji Rasheeda Adamu Abdullahi Maisa’a.

Karanta Wannan  Ku daina Rige-Rigen zuwa kasashen waje neman aiki, Ku tsaya mu gyara kasa>>Shugaba Tinibu ya roki Matasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *