Tuesday, February 3
Shadow

Babu wata data fita daga Musulunci zuwa Kirista>>Gwamnatin Jihar Zamfara

Gwamnatin Zamfara ta karyata labarin dake cewa wata me suna Zainab ta fita daga Musulunci zuwa Kirista a jihar.

Me magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Yace sun yi bincike ta hanyar kiran Alkalin Alkalai na jihar da kiran dukkan masu ruwa da tsaki na jihar kan bangaren shari’a duk sun tabbatar musu babu wata me suna Zainab data canja addini.

Dan haka ya bayyana cewa labarin karyane wadda wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa dan neman mabiya.

Karanta Wannan  Motar da Kashim Shettima ya baiwa Adam A. Zango Zalunci ne>>Inji Malam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *