
Hadimin tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari watau Bashir Ahmar yawa wani da ya zargeshi da siyasantar da mutuwar Buhari da cewa, Allah ya isa.
Bashir Ahmad dai ya wallafa damuwa kan yanda wasu jam’iyyun siyasa suka fara siyasantar da mutuwar Buhari inda yace hakan bai dace ba yayin da ko kwanaki 7 ba’a yi da mutuwar Buharin ba.
Saidai a martanin da wani ya masa yace “Kaima fa Bashir wallahi baka respecting mutuwar buhari kawai foarming engagement kake which is very unfortunate nazaci zakayi neman engagement dakomai amma banda mutuwar it’s shame wallahi”
Bashir ya bashi Amsar cewa
“Allah yayi min hisabi tsakanin ni da kai. Ban yafe wannan mummunar maganar da ka dora min ba.”
Saidai ya sake baiwa bashir amsar cewa “Indai sharri nama Allah yasakama tweet dim dakayi akan peter obi kawai ma abun kunyane kaida kake zaman karbar ta, aziyyar mutumin dayafi komai mahimmanci arayuwarka amma kanacewa wai yanemi hadin kanka kowa inzai mutu kayi siyasa da mutuwarsa amma banda buhari gaskiya ce.”