
Bankin Duniya yace kusan rabin ‘yan Najeriya sun fada cikin talauci tsamo-tsamo saboda tsadar rayuwa dake karuwa akasar.
Sanarwar da bankin ya fitar yace kaso 46 na ‘yan Najeriya watau mutane Miliyan 107 sun fada cikin talauci inda suke rayuwa a kasa da Dala $2.15 a kullun.
Bankin yace ma’aikata basa samun rayuwa me kyau saboda Albashinsu baya kai musu yanda ya kamata.
A baya dai bankin yace akwai Talauci sosai a tsakanin kauyawan Najeriya.