
Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa, Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ce gwamnati da aka taba yi wadda sam bata da kunya.
Jam’iyyar ta bayyana hakane ta bakin me magana da yawunta, Bolaji Abdullahi.
Yace wani abin mamaki shine yanda da jin jita-jita cewa ‘yan Adawa na jam’iyyar ADC zasu koma Jam’iyyar PRP, har an samu wasu masu ikirarin shugabancin jam’iyyar PRP sun bayyana.
Yace Gwamnatin tarayya da APC zasu ci gaba da karyata cewa, basu da hannu a irin wadannan abubuwan amma Duniya tana ganin abinda ke faruwa.