Tuesday, February 3
Shadow

Bayan da Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya baiwa Adam A. Zango mota, Shima Musa Mai Sana’a yace yana mika kokon bararsa wajan Kashim

Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana’a ya bayyana cewa yana mika kokensa ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima akan cewa ya yiwa APC wahala amma har yanzu ba’a bashi komai ba.

Ya bayyana cewa, dashi aka yi yakin neman zabe da komai amma ko sannu babu wanda yace masa.

Dan haka yace yasan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima mutum me me tausai shiyasa yake mika kokon bararsa a wajansa.

@maisanaakanotv

fatan alkairi masoyana naku musa Abdullahi mai sana,a kano nagode sosai

♬ original sound – musa Maisana,a

Ya bayyana hakane bayan da Mataimakin shugaban kasar ya baiwa abokin aikinsa, Adam A. Zango kyautar mota ta Naira Miliyan 80.

Karanta Wannan  An zargi cewa An fifota baiwa Adam A. Zango kulawa fiye da sauran wadanda suka yi Hadari tare a Asibiti inda aka bar su duk da sun fi shi jin jiki, har daya ta rasu daga ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *