Sunday, June 1
Shadow

Bayan da ta zargeni da nemanta da lalata Har Hotunan Selfie Sanata Natasha Akpoti ke daukar mu ni da ita idan mun tafi aiki, saboda tsabar jin dadin aiki dani kuma nace ta kawo hujjar zargin da take min amma taki

Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, Abin mamaki bayan da sanata Natasha Akpoti ta zargeshi da cewa ya nemeta da lalata, sun yi tafiye-tafiye tare har zuwa kasashen waje aiki.

Yace kuma har hotuna Selfie take daukarsu idan suna aiki saboda jin dadin aiki dashi.

Yace amma kuma ya nemi ta gabatar da hujjar zargin da take masa amma taki.

Sanata Natasha Akpoti dai tace ba zata bayar da hujjojin zargin da takewa, Sanata Godswill Akpabio ba sai an je kotu.

Karanta Wannan  Ni 'yan uwana ba 'yan gargajiya bane kuma ni gyaran tarbiyya nake>>Martanin GFresh Al-amin ga wanda kw cewa shima 'yan uwansa su zaneshi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *