Rahotanni daga Fakistan na cewa, Kasar India ta jefa mata makami inda ya kashe yaro ya jikkata mutane 2.
Lamarin na zuwane yayin da ake tsaka da yakin cacar baki tsakanin kasashen biyu.
Saidai da yawa sun ce India ta yi gaggawar kaiwa Pakistan harin.
Wasu rahotanni dai sun ce Pakistan din ta sha Alwashin yin ramuwar gayya.
Kasar ta Pakistan ta sanar da kulle sararin samaniyar ta na tsawon awanni 48 inda tace tana shirin kai harin ramuwar gayya.
Tuni shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana rashin jin dadin lamarin inda yace yana fatan kasashen zasu yi sulhu.