
Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu ta bayyana cewa, akwai sanda ake ta son aurenta amma bata maida hankali ba.
Tace amma yanzu ta na son ta yi aure kamin komawa ga mahaliccinta.
Ummi ta bayyana hakane a sabuwar hirar da BBChausa ta yi da ita inda tace ko makiyinta bata son ya shiga wahala rayuwar data shiga.
Saidai Ummi tace ida kuma Allah ya kaddaro cewa a haka zata mutu ba tare da yin aure ba, zata rungumi kaddararta.
An fara jin halin da Ummi ke ciki nw bayan hirar da Hadiza Gabon ta yi da ita a shirin ta na Gabon Show da ta ke yi a YouTube channel dinta.
Da yawa dai sun tausayawa Ummi Nuhu inda aka rika tara mata kudi.