Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar Hisbah dake Kano ta Hafsat Baby wadda aka fi sani da hafsa Lawancy ‘yar Tiktok wadda Bidiyon tsiraicinta ya bayyana.
A wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga Hafsat da wasu sauran mata a tsugune a ofishin Hisbah.
Tuni shugaban hukumar ta Hisbah ta Kano,Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar da kama Hafsat baby.
A wasu Rahotannin dai,Hafsat ta bayyana cewa, itace a bidiyon kuma ita ta dauki kanta bidiyon amma ta ajiye a wayarta, bata san wanene ya turawa Duniya ba.
Tace ba ta turawa kowa Bidiyon ba.