Friday, December 5
Shadow

Binani ta ƙara sayo sabon jirgi domin fara jigilar fasinja

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Kamfanin Sufurin Binani Air mallakin tsohuwar ƴan takarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023 Sanata Aishatu Ɗahiru Binani ya ƙara sayo sabon jirgi a shirye-shiryen shi na fara aikin jigilar fasinja a Najeriya.

Binani Air wanda ya samu lasisin fara wannan aikin lokacin ɗaya da kamfanin sufurin Rano Air, Hausa Daily Times ta gano kamfanin ya samu jinkirin fara wannan aikin a sakamakon wasu dalilai da ba kowa ya sani ba amma dai ana ganin bai rasa nasaba da rashin ƙarasowsn sauran jiragen da ya saya daga ƙasashen waje.

Ga ma’abota yawan tafiye-tafiye ta filin jirgin Nnamdi Azikiwe International na Abuja sun jima su na ganin jirgin farko da kamfanin ya fara kawowa ajiye, to sai dai yanzu kamfanin ya ƙara kawo na biyu wanda ya kai ga adadin jiragen su ka zama guda biyu.

Karanta Wannan  An kama wannan mutumin ya saci kwalayen sigari guda 9 daga wani Super Market wanda darajarsu ta kai Naira Dubu 90

Da waɗannan jiragen, ana kyautata zaton nan ba da jimawa ba Binani Air zai soma aiki domin shiga ya yi gogayya da sauran kamfanonin sufurin sama a Najeriya.

Wani fata ku ke wa wannan kamfani a daidai lokacin da fannin sufurin jiragen sama ke fama da ƙalubale?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *