Wednesday, March 18
Shadow

Burkina Faso ta haramta auren jinsi

Gwamnatin sojin Burkina Faso a ƙarƙashin jagorancin Faso Ibrahim Traore ta sanar da haramta auren jinsi a ƙasar baki ɗaya.

Wannan na zuwa ne kimanin shekara guda bayan an amince da wani daftarin dokoki da aka yi garambawul a kan dokokin iyalin ƙasar, inda a ciki aka ƙara auren jinsi.

Ƙasar da ke yankin Sahel ta kasance a cikin ƙasashen Afirka 22 a cikin 54 da suka amince da auren jinsi, lamarin da ke ɗaukar hukuncin kisa ko zaman gidan kaso mai tsaro a wasu ƙasashen.

A jiya Litinin ne gwamnatin ƙasar ta amince da sabuwar dokar wadda ta haramta auren na jinsin.

A sabuwar dokar, wanda aka kama da auren jinsi zai iya fuskantar zaman gidan yari na shekara biyar, kamar yadda ministan shari’a na ƙasar Edasso Rodrigue Bayala ya sanar a kafar gwamnatin ƙasar ta RTB.

Karanta Wannan  Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello da EFCC ke bincike kan zargin Satar Naira Biliyan 80 yace shugaba Tinubu ba sai ya je jikar Kogi yakin neman zabe ba, ya ci zaben 2027 a jihar

A bara ma dai maƙwabciyar ƙasar, Mali ta yi dokar haramta auren jinsi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *