Amfanin tuwon masara
Anan zamu yi magana akan amfanin garin masara da kuma tuwon masara a hade.
Garin Masara yana maganin gudawa sosai, hakan yana faruwane saboda fiber ko dusa dake cikinsa.
Yana Taimakawa narkewar abinci a cikin mutum.
Idan mutum na fama da kashi me tauri ko kuma yana hawa bandaki ya kasa yin kashi, garin masara ko tuwo yana taimakawa sosai.
Garin masara ko Tuwo yana taimakawa sosai wajan rage kiba.
Garin Masara da tuwo suna maganin ko taimakawa me ciwom zuga.
Garin masara ko tuwo yana maganin kumburin jiki.
Garin masara ko Tuwo yana maganin yunwa, bayan tuwo, ana iya yin burodi dashi ko a barbada akan abinci irin su dangin cake da sauransu a ci.