Basir ga mai ciki
Basir ga mata masu ciki ba sabon abu bane, wani bincike ya gano cewa,duk cikin mata masu ciki 3 ana samun macen dake da basur 1.
Mata masu ciki na fama da basir saboda yanda jikinsu ke budewa dalilin daukar ciki da nauyin dan suke dauke dashi.
Yawanci basir din mata masu ciki yana farawa ne a yayin da cikin ya fara nauyi,watau daga wata na 3 zuwa sama.
Masana kiwon lafiya sun bayar da shawarar cewa,idan a baya kin taba cin basir yayin da kike da ciki,yana da kyau ki nemi shawarar likita a yayin da kika kara samun ciki.
Maganin basir ga mai juna biyu
Ga hanyoyin magance basir ga mai juna biyu kamar haka:
A canja tsarin cin abinci: Canja tsarin cin abinci ta yanda za'a rika cin abinci me dauke da fiber,watau dusa, da kuma abinci me ruwa-ruwa, da shan ruwa akai-akai zasu tai...