Abin Kunyane hukuncin da kotu ta yanke a Kano>>Inji Babban Lauya, Femi Falana
Babban kauya, Femi Falana ya bayyana cewa, abin munyane hukuncin da kotu ta yanke a Kano.
Yace babbar kotun tarayya dake Kano bata da hurumin shiga harkar siyasar sarauta, hurumin kotun jiha ne.
Yace kuma hukuncin da kotun ta yanke ya kawo rudani dan bai fito da hukuncin da kotun ke nufi ba baro-baro.
Ya kara da cewa kotun daukaka kara ce dama dai take warware irin wannan matsala kuma yana da kyau ganin cewa yanzu an aikawa kotun daukaka kara shari'ar.