Majalisar Dattijai ta bayyana cewa, 'yan Bindiga da suka yi garkuwa da daliban makarantar MAGA dake jihar Kebbi, tserewa suka yi da suka ga jami'an tsaro.
Me magana da yawun majalisar, Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai.
Yace ba'a biya kudin fansa ba kamar yanda ake yamadidi.
Yace kuma wai dan ba'a ga an kama kowa ba ko ba'a ga gawar wadanda suka yi garkuwa dasu din ba, hakan ba yana nufin ba'a yi fadan ba.
Yace sannan kuma Ba dole bane sai jami'an tsaro sun sanar da yanda suka kubutar da daliban ba, kawai dai ana son a kubutar dasu kuma an kubutar dasu din.
Me magana da yawun Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Daha Al'Azhari ya bayyana cewa, malam ya bayyana musu sanda zai bar Duniya tun yana raye.
Yace ya gaya musu hakane tun kusan shekaru 10 da suka gabata.
Ya bayyana cewa malam ya bayyana musu cewa ba zai zarta shekaru 102 a Duniya ba. Yace kuma hakan ta tabbata inda yace watanni kadanne suka rage bai karasa hakan ba.
Yace wannan ba karamar karama bace.
https://www.tiktok.com/@sus__ride/video/7577694759100091656?_t=ZS-91mGaufAxOL&_r=1
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar yaki da rashawa da cin hanci EFCC ta gayyaci tsohon babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami.
Malami ne da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta.
Ya kuma tabbatar da cewa, zai amsa wannan gayyatar saboda ya yadda da bincike kuma shi dan kasa ne me bin doka.
Dalibin Marigayi, Dr. Idris Dutsen Tanshi, Malam Ibrahim Matayassara ya bayyana cewa, ba'a wa dan bidi'a Addu'a idan ya rasu.
Malamin ya bayyana cewa saidai ace sannun mu dai.
Ya soki Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami saboda yin ta'aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Ya kira Malam Pantami da Munafiki inda yace ba zai samu kujerar siyasar da yake nema ba.
https://www.tiktok.com/@officialmustymodawa/video/7577651549132819719?_t=ZS-91mAOPyU25Y&_r=1
Wata matashiya daga jihar Sokoto ta yi Allah wadai da masu gidajen haya saboda tsadar da gidajen hayar suka yi.
Tace matasa basa iya yin aure saboda tsadar gidajen haya a Sokoto inda tace gidan haya sai daga Naira Miliyan 1 zuwa sama.
Ta ce hakan yasa 'ya'yan talakawa da yawa sun koma Mazinata inda tace dan haka in Allah ya yarda masu gidajen haya suma sai 'ya'yansu sun koma mazinata.
https://www.tiktok.com/@safrat.muhammad.h/video/7577449793216089352?_t=ZS-91m8feL96yf&_r=1
Wannan wata matashiyace da ta sha da Kyar a hannun masu kwacen waya a Kano.
Rahotanni sun ce ta ki yadda ta basu wayar inda suka yanke ta a wiya, amma yankan bai shiga ba sosai.
Daga karshe dai ta sha da wayarta amma sun ji mata ciwo a wuya.
https://www.tiktok.com/@washaummi258/video/7577539322400869639?_t=ZS-91m7c3UjHNY&_r=1
Malamin Addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami ya tabu sosai da rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Bayan Wallafa sakon ta'aziyya da yayi, ya kuma wallafa wani tsohon Bidiyon da suke tare da Dahiru Bauchi inda yaje gaisheshi.
A yau ne dai bayan Sallar Juma'a ake sa ran yiwa gawar Marigayin Sutura a kaishi makwancinsa.
https://twitter.com/ProfIsaPantami/status/1994113635749429565?t=ByzUyOljGKR-diBRuGR2uA&s=19
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta hana 'yan kasashe Matalauta zuwa kasar Amurka cirani.
Yace wannan hanin zai yi shine na dindindin.
Ya bayyana hakane Ranar Alhamis a wani sako da ya fitar na shirin bukukuwan karshen shekara.
Shugaba Donald Trump na daga cikin tsarinsa na hana baki shiga kasar Amurka.
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya bayyana cewa, shi ko nawa za'a biyashi ba zai iya aikin soja ba.
Yace dalili kuwa shine ba ya son ya mutu a irin wannan hayar ba saboda ko ya mutu babu wanda zai san darajarsa.
Ya bayar da misalin cewa, yanzu ga gawar Janar can watau(Brigadier Mohammed Uba) a daji har yanzu ba'a dawo da ita ba.
https://twitter.com/channelstv/status/1994113706431496508?t=qyEyfHxF69l_yfczxx6Now&s=19