Wednesday, February 25
Shadow

Duk Labarai

Kowa ya Kwantar da Hankalinsa: Trump bai isa ya kawo Khari Najeriya ba sai na amince>>Inji Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Kowa ya Kwantar da Hankalinsa: Trump bai isa ya kawo Khari Najeriya ba sai na amince>>Inji Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa Amurka bata isa ta kawo Hari Najeriya ba sai da amincewarsa. Ya bayyana hakane ta bakin me bashi shawara kan sadarwa, Daniel Bwala a hirarsa da manema labarai. Daniel Bwala yace Keta dokar kasa da kasa ne wata kasa ta kaiwa wata kasa hari ba tare da sanin kasar da aka kaiwa harin ba. Yace ba'a fahimci abinda Trump ya fada bane, wannan abu ne da zasu warwareshi ta hanyar Diplomasiyya. Ya bayyana cewa, Suna godiya ga Trump da amincewa da yayi ya sayarwa da Najeriya makamai a zamanin mulkinsa na farko.
Kalli Bidiyon: Wai ku ‘yan Najeriya kun rainamu koh, kuna ganin ba zamu iya da sojojin Amurka ba? To Wallahi Kharo da kaiy kawai idan nawa Sojan Amurka ko shurhawa ba zai yi ba>>Inji Wannan sojan Najeriyar

Wani sojan Najeriya ya bayyana yana cewa, 'yan Najeriya su daina musu kallon ba zasu iya da sojojin kasar Amurka ba. Yace Karo da kai kawai idan yawa sojan Amirka ko shurawa ba zai yi ba. Yace su da ake kaisu kasashe su taimaka wajan samun zaman Lafiya shine za'a ce wai wata Amurka zata gagaresu? Yace mutane su daina wannan tunanin: https://twitter.com/AsakyGRN/status/1985323453948321847?t=aeOzMrIF9t_KuYK8xXj7Hg&s=19
Wallahi Sharri aka kala min ban zaghi Shugaban Amurka, Donald Trump ba, Inji Sanata Godswill Akpabio bayan da wani Rahoto ya bayyana dake cewa ya gayawa Trump maganganu marasa dadi

Wallahi Sharri aka kala min ban zaghi Shugaban Amurka, Donald Trump ba, Inji Sanata Godswill Akpabio bayan da wani Rahoto ya bayyana dake cewa ya gayawa Trump maganganu marasa dadi

Duk Labarai
Kakakin Majalisar Dattijai Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa sharri ake masa rahoton dake cewa wai ya zagi shugaban kasar Amurka Donald Trump. Rahotan wanda wata kafa me suna Rant HQ Politics ta wallafa tace Akpabio yace ai a Najeriya ake Shekye mutane ba'a Amurka ba dan haka Ba ruwan Trump da Najeriya. Saidai a sanarwar daya fitar, Akpabio yace shi bai fadi wannan magana ba, sharri aka kala masa. Akpabio yace yana girmama Trump a matsayin shugaban kasa me karfi sannan ba zai tsoma bakinsa akan abinda ke faruwa a kasar Amurka ba.
Kalli Bidiyon: Dan Allah a samu malaman (Gaskiya) su fito su yi bayani, Samarin mu sun dauki fatawar Sheikh Karmawi, idan suka zo neman auren mu sai su ce wai sai sun leka>>Inji Murja Kunya

Tauraruwar Tiktok Murja ta bayyana cewa suna neman Agaji daga malamai su fito su fayyace maganar Sheikh Alkarmawi wanda yace ya halasta idan mutum ya je neman aure a bude masa ya leka. Murja tace samarinsu sun damesu duk wanda yaje sai yace malam yace a rika lekawa. Tace dan Allah a samu wani malami ya fito yayi bayanin gaskiyar lamarin. https://www.tiktok.com/@murjakunya0/video/7567958837995654456?_t=ZS-915ifq9Co1Q&_r=1
Fadar Shugaban kasa ta karyata Rahoton dake cewa, Shugaba Tinubu zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump

Fadar Shugaban kasa ta karyata Rahoton dake cewa, Shugaba Tinubu zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta musanta Rahoton dake cewa shugaban kasar zai gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Wani Rahoto da Sahara Reporters suka ruwaito sun ce sun samu daga fadar shugaban kasa cewa shugaba Tinubu zai gana da mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance a ziyarar da zai kai kasar. Saidai fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tace ba gaskiya bane, kuma idan ma shugaba Tinubu zai je kasar Amurka, da shugaban kasar, Donald Trump zai gana ba da mataimakinsa ba.
Da Duminsa: Kasar Chadi ta kulle iyakarta da Najeriya bayan rahotan cewa Amurka zata kawo Khari Najeriya

Da Duminsa: Kasar Chadi ta kulle iyakarta da Najeriya bayan rahotan cewa Amurka zata kawo Khari Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Chadi na cewa, kasar ta kulle iyakokinta da Najeriya bayan bayyanar Rahoton cewa Amurka na iya kawo Hari Najeriya. Kafar Zagazola Makama ce ta ruwaito cewa shugaban soji na kasar Chadi Muhammad Idris Derby Itno ne ya bayar da wannan sanarwar. Yace sojojin kasarsa su tare iyakar kasar da Najeriya saboda ana tsammanin 'yan Bindiga zasu iya tserewa can yayin da Amurka ke shirin kawo hari Najeriya. Hakanan sanarwar tace kasar Chadi ba zata bari wasu 'yan kasar waje su shigar mata kasa ba.
Kalli Bidiyo: Sai mun yi Hakuri da Fulani makiyaya, dalili kuwa shine su a wajansu sun fi son Saniyarsu fiye da ransu, bama wani ba, Haka Allah ya haliccesu>>Inji Sanata Aishatu Dukku

Kalli Bidiyo: Sai mun yi Hakuri da Fulani makiyaya, dalili kuwa shine su a wajansu sun fi son Saniyarsu fiye da ransu, bama wani ba, Haka Allah ya haliccesu>>Inji Sanata Aishatu Dukku

Duk Labarai
Sanata A'ishatu Dukku ta bayyana cewa bata san dalilin da yasa mutanen Najeriya suka canja ba, tace ko da saboda magin da ake sha ne? Tace Bafulatani Allah ya halicceshi ne shi yana son Saniyarsa fiye da yanda yake son kansa bama wai wani ba. https://twitter.com/General_Somto/status/1984916062287147309?s=19 Ta bayyana hakane a zauren majalisar Dattijai yayin da ake tattauna maganar hare-haren da Fulani Makiyaya ke kaiwa manoma.
Hankalin ‘yan Kudu ya tashi sosai suna fadar ashe satar mai zai kawo ku? Bayan da aka bayyana Jihar Rivers a matsayin inda sojojin Amurka zasu sauka idan sun zo Najeriya

Hankalin ‘yan Kudu ya tashi sosai suna fadar ashe satar mai zai kawo ku? Bayan da aka bayyana Jihar Rivers a matsayin inda sojojin Amurka zasu sauka idan sun zo Najeriya

Duk Labarai
Wani bature me suna Dr. Walid Phares ya bayyana cewa, yana bayar da shawara ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya girke sojojin kasar Amurka a Birnin Fatakwal na Jihar Rivers inda yace ta nan ne za'a rika samun damar kai kayan agaji daga Choci-Choci na Duniya. Saidai wannan magana batawa 'yab kudu da yawa dadi ba musamman ma 'yan Jihar ta Rivers inda suke cewa ba yakar matsalar tsaro zata kawo Amurka Najeriya ba, Satar mai ne zai kawo su. Shugaban kasar Amurka, Donald Trump dai ya bayyana aniyarsa ta son Afkawa Najeriya da hare-hare da sunan yaki da masu yiwa kiristoci Khisan Kyiyashi.
Wani Bature me fada a ji yayi kira ga Trump ya tabbatar da Kafuwar kasar Biafra

Wani Bature me fada a ji yayi kira ga Trump ya tabbatar da Kafuwar kasar Biafra

Duk Labarai
A yayin da ake tsaka da tattauna barazanar shugaban kasar Amurka Donald Trump ta kawo hari Najeriya da sunan cewa zai baiwa kiristoci kariya daga Khisan Khiyashi da ake musu. Wakili a kungiyar tsaron kasashen Turawa ta NATO me suna Gunther Fehlinger yayi kira ga Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya tabbatar da kafuwar kasar Biafra. https://twitter.com/GunterFehlinger/status/1985252165066092817?s=19 Hakan yasa masu sharhi da yawa ke bayyana cewa, dama abinda ya tado da maganar cewa ana yiwa Koristoci khisan Kyashi kenan ana son kafa kasar Biafra ne.