Saturday, December 13
Shadow

Duk Labarai

Rundunar sojin ruwan Najeriya za ta kafa sansani a Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya za ta kafa sansani a Kebbi

Duk Labarai
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a garin Yauri na jihar Kebbi a wani mataki na bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa. Matakin na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami'an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin jihar Kebbi a ranar Alhamis. Tawagar ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu - wanda ya wakilci babban hafsan sojin ruwan ƙasar ta ziyarci Kebbi ne domin duba yadda za ta samar da sansaninta a jihar. Rundunar ta ce ta ɗauki matakin ne domin faɗaɗa ayyukanta zuwa sauran yankunan ƙasar, musamman domin samar da tsaro a kan iyakokin ƙasar na tudu da na ruwa domin magance ayyukan ɓata-gari a kogin Niger. “Duk da irin muhimmanci da kogin Niger ke da shi wajen haɓaka ayyukan noma da samar da lantarki da kamun kifi da sauran sana'o...
Tinubu ya nemi gwamnoni su haɗa hannu don yaƙi da talauci a ƙauyuka

Tinubu ya nemi gwamnoni su haɗa hannu don yaƙi da talauci a ƙauyuka

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin ƙasar su fitita walwalar ƴan Najeriya ta hanyar zuba jari a ƙauyuka da yankunan karkara, ta hanyar bunƙasa wutar lantarki da ayyukan noma domin kawar da talauci. Kiran na zuwa ne bayan gabatar da wani shirin gwamnati na musamman kan bunƙasa tattalin arziki a matakin mazaɓu da aka yi wa laƙabi da 'Renewed Hope Ward Development Programme (RHWDP)' da ministan kasafi da tsare-tsare na ƙasar ya yi a lokacin taron majalisar tattalin arzikin ƙasar. Manufar sabon shirin na RHWDP shi ne tabbatar da bunƙasar tattalin arziki ta hanyar taimaka wa mazaɓun ƙasar 8,809 a faɗin jihohin ƙasar 36, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana. Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci gwamnonin ƙasar su yi duk mai yiwuwa wajen tallafa wa rayukan...
Ƴansandan Kaduna sun kama mai kwaikwayon muryoyin gwamnoni

Ƴansandan Kaduna sun kama mai kwaikwayon muryoyin gwamnoni

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta kama wani matashi da ya ƙware wajen kwaikwayon muryoyin wasu gwamnonin Najeriya. Ƴansandan na zargin matashin da amfani da muryoyin wajen damfarar mutane maƙudan ƙuɗaɗe. Kakakin rundunar ƴansandan jihar ASP Mansur Hassan, ya shaida wa BBC cewa dama rundunar ƴansandan jihar ta jima tana neman matashin ruwa a jallo. ''Bayan kama shi mun same shi da lambobin waya da dama ciki har da na manyan mutane a ƙasar nan'', in ji kakakin ƴansandan. ''Mutumin ya ƙware sosai wajen kwaikwayon muryoyin mutane, duk wani mutum da ba ka tunani zai iya yi maka muryarsa'', in ji shi.
Kalli Bidiyo: Habiba tace Duniya ba wanda take so sai Oga Sani bayan da ta ga Zqrmqlulunsalq

Kalli Bidiyo: Habiba tace Duniya ba wanda take so sai Oga Sani bayan da ta ga Zqrmqlulunsalq

Duk Labarai
Wata me Tiktok, Habiba ta bayyana cewa, Oga Sani take so da aure. Oga Sani wani ne da 'yar Tiktok, Shalele ta wallafa Bidiyonsa tsirara inda har al'aurarsa aka gani. Kuma tuni ake ta magana akansa. Saidai Habiba ita tace ta ji ta gani shi takeso. https://www.tiktok.com/@habibayarbaba/video/7533526686520855813?_t=ZS-8yVqJ2eyPhY&_r=1 Da yawa dai sun ce taga al'urarsa ne shiyasa take sonsa.
Kalli Bidiyo: Yanda ‘yan Fim suka gudanar da Shagali na musamman dan murnar kammala jinyar Adam A. Zango

Kalli Bidiyo: Yanda ‘yan Fim suka gudanar da Shagali na musamman dan murnar kammala jinyar Adam A. Zango

Duk Labarai
Taurarin fina-finan Hausa sun shirya Shagali na musamman dan murnar warkewar abokin aikinsu, Adam A. Zango bayan Hadarin motar da ya rutsa dashi. An ga Adam A. Zango a wajan shagalin yana ta murmushi, kuma an ga Abokan sana'ar sa da yawa da suka https://www.tiktok.com/@kannywoodtv1/video/7533510233835031830?_t=ZS-8yVoIu1I0TA&_r=1
Kalli Bidiyo: Wallahi Shehu Tijjani ya ga Manzon Allah, gani na Zahiri, ta hanyar Ilimi da karamarsa>>Inji Imam Junaidu

Kalli Bidiyo: Wallahi Shehu Tijjani ya ga Manzon Allah, gani na Zahiri, ta hanyar Ilimi da karamarsa>>Inji Imam Junaidu

Duk Labarai
Malamin Darika, Imam Junaidu ya bayyana cewa wallahi Shehu Tijjani ya ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). Ya bayyana hakane a daya daga cikin Bidiyon sa na wa'azi. Malam yace ana ganin Annabi ta hanyar Ilimi da Karama. https://www.tiktok.com/@abdu_rashid_khalid_tanut/video/7533430142706781445?_t=ZS-8yVmrPit6Bc&_r=1 me zaku ce?
‘Yan kasuwar man fetur sun yi gargadin Dagote zai kawo rudani a kasuwar man fetur idan ya kaddamar da aniyarsa ta fara jigilar man fetur dinsa zuwa gidajen mai

‘Yan kasuwar man fetur sun yi gargadin Dagote zai kawo rudani a kasuwar man fetur idan ya kaddamar da aniyarsa ta fara jigilar man fetur dinsa zuwa gidajen mai

Duk Labarai
Kungiyoyin 'yan kasuwar Man fetur, NOGASA, PETROAN sun bayyana rashin jin dadinsu da yunkurin Aliko Dangote na fara kai man fetur din zuwa gidajen mai da motocinsa na jigilar da ya siyo. 'yan kasuwar sun ce Dangote ba zai iya yin wannan aiki shi kadai ba. Sun ce idan kuwa yace zai yi, to zai kawo rudani ne a kasuwar man fetur din. Kungiyoyin sun koka da cewa, Dangote ya dauki wannan mataki ne ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki a harkar ba. Sun yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya shiga maganat. Shugaban NOSAGA, Bennett Korie ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis a wajan babban taron kungiyar. Shima Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry ya jadada hakan. Saidai a martanin matatar Dangote, tace 'yan kasuwar suna wannan babatu ne kawai dan basu son ci g...
Kalli Bidiyo: Nima nace Shugaba Tinubu ya rigamu gidan gaskiya, wanda ya fasa kamani Allah ya tsin masa>>Inji Sheikh Salihu Zaria

Kalli Bidiyo: Nima nace Shugaba Tinubu ya rigamu gidan gaskiya, wanda ya fasa kamani Allah ya tsin masa>>Inji Sheikh Salihu Zaria

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Salihu Zaria ya nuna bacin ransa kan kamun da akawa me watsa labarai a kafar Tiktok, Sultan. Malamin yace shima ya fada cewa shugaban kasa ya mutu kuma wallahi sai ya mutu din ma. Yace wanda ya fasa kamashi Allah ya tsine masa Albarka. Malam yace ga wadanda ke haifar da matsalar tsaro nan ba'a kamasu ba sai Sultan. Kalli Bidiyonsa a kasa: https://www.tiktok.com/@saleemyusufmuhammadsambo/video/7533340465458908472?_t=ZS-8yVSPtBKLon&_r=1 Kama Sultan ya jawo cece-kuce da Allah wadai sosai ga gwamnatin Tinubu.
ADC ba barazana bane: Cikin Sauki Tinubu zai samu kuri’u Miliyan 15 a zaben 2027 ya lashe zabe>>Inji wani na hannun damar shugaban kasar

ADC ba barazana bane: Cikin Sauki Tinubu zai samu kuri’u Miliyan 15 a zaben 2027 ya lashe zabe>>Inji wani na hannun damar shugaban kasar

Duk Labarai
Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Nicolas Felix ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai samu kuri'u Miliyan 15 a zaben 2027. Yace wannan babu tantama akai. Ya bayyana hakane a yayin da ya rabawa wasu mabukata man fetur kyauta a Suleja dake jihar Naija ranar Alhamis. Ya ce Hadakar 'yan Adawa a ADC ba zata zamarwa Shugaba Bola Ahmad Tinubu barazana ba. Ya kara da cewa, kamar yanda 'yan Adawar suka taho suka hadu, haka kuma zasu watse.