Monday, November 23
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa:Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya aikawa kotu da korafi kan wata Mugunta da take hakkinsa da ake masa a ofishin ICPC

Da Duminsa:Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya aikawa kotu da korafi kan wata Mugunta da take hakkinsa da ake masa a ofishin ICPC

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya aikewa da kotun Magistrate dake Abuja da korafin cewa, ana kokarin take masa hakkinsa a matsayinsa na dan kasa. ElRufai yayi zargin cewa, shugaban Hukumar ICPC din Musa Adamu Aliyu ta hannun wasu yaransa ya bayyana masa cewa sharadin sakinsa shine sai idan ya amince zai daina shiga harkar siyasa. El-Rufai ta hannun Lauyansa yace wannan kokarine na take masa hakkinsa a matsayinsa na dan kasa wanda ba zai lamunta ba. Zuwa yanzu dai Hukumar ta ICPC bata ce uffan ba kan zargin da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mata.
Tauraruwar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj zata maka wani dan Najeriya a kotu saboda ya ce mata tsohuwa

Tauraruwar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj zata maka wani dan Najeriya a kotu saboda ya ce mata tsohuwa

Duk Labarai
Tauraruwar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj ta bayyana shirin maka wani dan Najeriya a kotu saboda ya ce mata tsohuwa. Nicki Minaj ta bayyana hakane bayan da mutumin me suna Dr. Penking ya bayyana ta a matsayin 'yar shekaru 43 wadda kuma ta tsufa. Inda ya kara da cewa ya kamata ta daina waka. https://twitter.com/i/status/2032753621310283913 Saidai abin bai mata dadi ba Da farko dai ta yiwa Lauyanta magana inda tace zasu saka dan Najeriyar cikin wanda zasu yi kararsu, saidai daga baya ko mi ta gani sai ta goge sakon. Saidai shi dan Najeriyar yace a shirye yake ya fuskanceta a kotu dan yana da 'yancin fadar Albarkacin bakinsa kuma ra'ayinsa ya bayyana. https://twitter.com/i/status/2033095286499770596
Kalli Bidiyon: An kawo min Naira Biliyan 500 in jagoranci malamai da zasu wa APC yaki  neman zabe amma nakiya>>Inji Sheikh Sanusi Kalil

Kalli Bidiyon: An kawo min Naira Biliyan 500 in jagoranci malamai da zasu wa APC yaki neman zabe amma nakiya>>Inji Sheikh Sanusi Kalil

Duk Labarai
Malamin addinin Islama, Sheikh Sanusi Kalil ya bayyana cewa an kawo masa tayin ya jagoranci malamai da zasu wa Gwamnatin APC yakin neman zabe a 2027. Yace an ware kudi Naira Biliyan 500 sannan duk wanda zai jagoranci tafiyar za'a bashi kawo me tsoka daga cikin kudin. Saidai malam yace bai yadda da wannan tayin ba. https://www.tiktok.com/@voice_of_muslims_91/video/7616871755725982997?_r=1&_t=ZS-94iDqqtUQsL
Kalli Bidiyon: Uban mu daya da Nazir Ahmad Sarkin Waka, Amma bai taba min Kyauta ba>>Inji Ibrahim Sinana

Kalli Bidiyon: Uban mu daya da Nazir Ahmad Sarkin Waka, Amma bai taba min Kyauta ba>>Inji Ibrahim Sinana

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Ibrahim Sinana ya bayyana cewa, Ubansu daya da Nazir Ahmad Sarkin Waka amma bai taba masa kyauta ba. Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da yake godewa Ali Nuhu bisa kyautar da ya masa da kuma kiran sunayen masu kudi a Kannywood wanda basa kyauta. https://www.tiktok.com/@ibrahimsinana5/video/7616759585499581714?_r=1&_t=ZS-94hnNVB8l6H