Saturday, February 14
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon kokarin da golan Senegal yayi da ya dauki hankula sosai

Kalli Bidiyon kokarin da golan Senegal yayi da ya dauki hankula sosai

Duk Labarai
Golan Senegal Yehvan Diouf wanda ke wajan fili yayin da ake wasa, ya rikewa bokin aikinsa tsumman goge zufa ya hana ma'aikatan Filin wasan daukarsa. A wani Bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga golan yana kokawa da ma'aikatan filin yayin da suke ta kokarin kwace tsumman daga hannunsa. https://twitter.com/i/status/2013065997125566495 A baya dai, An ga yanda ma'aikatan filin suka dauke tsumman na goge zufar golan Najeriya, Nwabali wanda hakan ya jawo cece-kuce sosai.
Mun basu aiki kuma sun yi aikin yanda ya kamata, Shugaban kasar Senegal bayan da suka dauki kofin AFCON

Mun basu aiki kuma sun yi aikin yanda ya kamata, Shugaban kasar Senegal bayan da suka dauki kofin AFCON

Duk Labarai
Shugaban kasar Senegal ya jinjinawa 'yan wasan kasarsa bayan da suka yi nasarar daukar kofin AFCON. Ya bayyana cewa sun basu aiki kuma sun gudanar da aikin yanda ya kamata. Senegal ta doke me masaukin baki, Morocco da ci 1-0 inda hakan ya bata damar lashe kofin na AFCON. Shugaban yace 'yan wasan nasa sun yi wannan nasara ne duk da kalubalen da suka rika fuskanta.
Kalli Bidiyon: Shima Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana’a ya samu gagarumar kyauta daga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Kalli Bidiyon: Shima Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana’a ya samu gagarumar kyauta daga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana'a ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya masa kyauta ta hannun Ali Nuhu. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya fito yakewa Ali Nuhu da mataimakin shugaban kasar godiya. Saidai be bayyana irin kyautar da aka masa ba https://www.tiktok.com/@maisanaakanotv/video/7596653199013022988?_t=ZS-93BDfn9OYTI&_r=1 A baya dai Musa Mai Sana'a ya fito yace ya kashe Miliyoyin Naira wajan yiwa Gwamnatin Tinubu hidima amma ba'a bashi komai ba. Hakanan Kashim Shettima yawa Adam A. Zango babbar kyauta ta mota.
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle zai aurar da ‘ya’yansa 9

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle zai aurar da ‘ya’yansa 9

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle zai aurar da 'ya'yansa maza da mata su 9. Katin gayyatar auren ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga cewa za'a yishi ne ranar 6 ga watan Fabrairu a babban masallacin Juma'a dake Abuja. Sunayen 'ya'yan nasa sune kamar haka, Ibrahim, Suraj, Safiya, Maryam, Aisha, Fahad, Muh’d, Nana Firdausi, and Farida. Kakakin jam'iyyar APC na jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kalli Bidiyon: Ku sakani a addu’a na karbi Addinin Musulunci >>Inji Wannan matar

Kalli Bidiyon: Ku sakani a addu’a na karbi Addinin Musulunci >>Inji Wannan matar

Duk Labarai
Wannan baiwar Allahn ta bayyana cewa ta karbi Addinin Musulunci inda ta nemi a sakata a addu'a. An ganta da litattafan Addinin Musulunci a Bidiyon data saki Kalli Bidiyon anan https://www.tiktok.com/@rejoiceallahnan0/video/7596051470563216657?_t=ZS-939pXUKkuDw&_r=1 https://www.tiktok.com/@rejoiceallahnan0/video/7596051470563216657?_t=ZS-939pXUKkuDw&_r=1
Kalli Bidiyon ‘yan kwallon Najeriya Super Eagles na maganar cewa ba’a biyasu hakokinsu ba kamin wasan da suka buga da Morocco

Kalli Bidiyon ‘yan kwallon Najeriya Super Eagles na maganar cewa ba’a biyasu hakokinsu ba kamin wasan da suka buga da Morocco

Duk Labarai
Wani sabon Bidiyon 'yan kwallon Najeriya, Super Eagles ya bayyana inda aka ji suna tattauna cewa ba'a biyasu hakkokinsu ba. An dauki Bidiyon ne kamin wasansu da Morocco wanda Moroccon ta fitar dasu a wasan Penalty. Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda ake dorawa hukumar NFF alhakin hakan. https://twitter.com/i/status/2012467439267717398