Tuesday, December 16
Shadow

Duk Labarai

Allah Sarki Kalli Bidiyon yanda aka cire hoton Ganduje daga ofishin APC ana maye da hoton sabon shugaban jam’iyyar

Allah Sarki Kalli Bidiyon yanda aka cire hoton Ganduje daga ofishin APC ana maye da hoton sabon shugaban jam’iyyar

Duk Labarai
A yayin da aka nada shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC bayan saukar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi. An ga Bidiyon yanda aka cire hoton Ganduje daga ofishin shugaban jam'iyyar aka mayeshi da na sabon shugaban jam'iyyar. https://twitter.com/INYAMURI/status/1939643637438267642?t=Pr0LkVz9nZOIaHCfud-I6A&s=19 Duniya kenan kowa da zamaninsa.
Kadaici na kai mutane 871,000 zuwa lahira duk shekara>>WHO

Kadaici na kai mutane 871,000 zuwa lahira duk shekara>>WHO

Duk Labarai
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO tace kadaici na kashe mutane 871,000 duk shekara. Rahoton yace a duk cikin mutane 6 na Duniya akwai mutum daya dake fama da kadaici wanda hakan ke haifar da cutuka kala-kala. Masanan sun ce, kadaici na kara hadarin kamuwa da shanyewar rabin jiki, da ciwon zuciya, da ciwon sugar da damuwa da kisan kai. Masana sun ce wayar hannu ta taimaka wajan saka mutane cikin kadaici inda ake samun karuwar masu kadaicewa da rashin son shiga mutane.
PDP na gudanar da manyan taruka biyu da nufin samo hanyar gudanar da taronta na NEC

PDP na gudanar da manyan taruka biyu da nufin samo hanyar gudanar da taronta na NEC

Duk Labarai
Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Najeriya na ci gaba da tattanawa wajen gani sun shawo kan ɓarakar da ta kunno kai a tsakaninsu da ya janyo tsaiko, wajen gudanar da taron majalisar zartawa na jam'iyyar da aka shirya gudanarwa a yau Litinin. Tun da safiyar yau ne dai aka ga jami'an 'yansanda da na tsaron fararen hula na Civil Defense suka yi wa ofishin jam'iyyar na Wadata Plaza, Abuja tsinke tare da hana dukkanin manyan jami'an jami'yyar shiga. Yanzu haka dai kwamitin amintanntu na jam'iyar na gudanar da wani taron sirri a babban ɗakin taro na Ƴar'adu Center da ke Abuja. Taron nasu na zuwa a daidai lokacin da gwamnonin jam'iyyar da ƴan majalisar dattawa da na wakilai da ke gudanar da wani taron a gidan gwamnatin jihar Bauchi da ke unguwar Asoko...
Rundunar ƴansandan Abuja ta musanta garƙame hedikwatar PDP

Rundunar ƴansandan Abuja ta musanta garƙame hedikwatar PDP

Duk Labarai
Newly deployed Nigerian Formed Police Unit (FPU) personnel under the African Union Mission in Somalia (AMISOM) arrive at Aden Abdulleh International Airport, Mogadishu, Somalia on January 6, 2016. AMISOM Photo / Ilyas Ahmed Rundunar ƴansandan Abuja ta musanta rahotannin da ke cewa jami'anta sun karɓe iko da hedikwatar jam'iyyar PDP ta Wadata Plaza a ranar Litinin. Rundunar ta ce tana son "ta nuna cewa babu gaskiya a rahotonnin sannan ba haka al'amarin yake ba. An kai jami'an ƴansandan ne zuwa wurin taron domin wanzar da doka da oda kamar yadda tsarin mulki ya tanada. A wata sanarwa, rundunar ta ce "babu wani lokaci da jami'an ƴansanda suka kulle sakateriyar jam'iyyar ta PDP." A sanarwar, kwamishinan ƴan sanda na Abujar ya buƙaci kafafen watsa labarai da su yi kaffa-kaffa wajen ...
Da Duminsa: ‘An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa gobe Talata’ Ji dalili

Da Duminsa: ‘An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa gobe Talata’ Ji dalili

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa. Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya tabbatar wa da BBC ɗage jana'izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina. ''Akwai ƙa'idoji da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana'iza a ƙasar, to yanzu haka ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,''in ji ministan. Mohammed Idris ya ce idan an kammala za a ɗauko gawar daga Hadaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Saudiyya. Ya ƙara da cewa tuni ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana'izar. Bayanai sun ce Alhaji Aminu Ɗantata...
Sai Mun yi nasara akan masu tada kayar baya dake fadin kasarnan>>Inji Hukumar Sojojin Najeriya

Sai Mun yi nasara akan masu tada kayar baya dake fadin kasarnan>>Inji Hukumar Sojojin Najeriya

Duk Labarai
Ya zama wajibi Nijeriya ta samu nasarar yaƙi da ƴan ta'adda — Hafsan Sojojin Kasa. Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa nasarar Najeriya kan ‘yan ta’adda da dukkan makiyan kasa tabbas ce. Janar Oluyede ya sake jaddada kudirin rundunar sojin Najeriya na kawar da ta’addanci tare da tabbatar da tsaron kasa ta hanyar dabarun yaki da ta’addanci masu inganci. Ya fadi hakan ne a yayin bikin addu’ar cocin addinai daban-daban da aka gudanar domin bikin ranar rundunar sojin kasa ta Najeriya na shekarar 2025 a ranar Lahadi a birnin Abuja. Ya kara da cewa sojin Najeriya ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kare ikon kasa da kuma kare ‘yancin dukkan ‘yan Najeriya. “Ba za mu taba barin darajar mu ba, wacce ke da nasaba da bangaskiyarmu, kuma za mu ci ga...
Yauce Ranar Kulle shafin  Facebook a Najeriya? Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

Yauce Ranar Kulle shafin Facebook a Najeriya? Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

Duk Labarai
A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta bai wa kamfanin Facebook na biyar tarar dala miliyan 290 bisa samun sa da laifin karya dokoki. A watan Yulin 2024 ne dai kotun ta umarci kafamin da ya biya tarar bayan samun shi da laifin taka dokokin da suka jiɓanci gasa da tallan haja da kuma na bayanan sirri. Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko kamfanin na Meta zai biya wannan tara da kuma matakin da gwamnatin ƙasar za ta ɗauka idan kamfanin ya gaza bin umarnin kotun. A watan Mayu ne kamfanin na Meta mamallakin Facebook ya yi barazanar rufe ayyukansa a Najeriya bisa abin da ya bayyana da tarar da ta wuce hankali. Wani rahoto ya nuna cewa al'ummar Najeriya ka iya rasa damar ci gaba da hulɗa da shafukan Facebook da Instagram idan dai har kamfanin na Meta ya aiwatar da barazanar da ya...
Jami’an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar Jam’iyyar PDP A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar Jam’iyyar PDP A Abuja

Duk Labarai
DA ƊUMIƊUMINSA: Jami’an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar Jam'iyyar PDP A Abuja. Daga Muhammad Kwairi Waziri A safiyar yau Litinin, an jibge jami’an tsaro a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Wadata Plaza, Abuja, gabanin babban taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) da aka shirya gudanarwa a yau. Jami’an ‘yan sanda, DSS da Civil Defence sun mamaye ko’ina a harabar ofishin jam’iyyar domin tabbatar da tsaro yayin taron, wanda ake ganin zai yanke muhimmiyar shawara kan makomar jam’iyyar da shugabancinta. Wata majiya daga cikin jam’iyyar ta bayyana cewa ana sa ran tattaunawa mai zafi kan shugabancin jam’iyyar na ƙasa, inda ake hasashen sauyin wasu muƙamai ko sabbin shawarwari game da tsarin PDP na gaba. Ana sa ran dattawan jam’iyyar, gwamnoni da wakilan PDP daga jihohi daban-daban za s...