Tuesday, March 3
Shadow

Duk Labarai

Ba zan iya sake jefa ‘yan Najeriya a wata sabuwar Wahala ba: Shugaba Tinubu ya soke karin kaso 5 akan kamfanonin Sadarwa

Ba zan iya sake jefa ‘yan Najeriya a wata sabuwar Wahala ba: Shugaba Tinubu ya soke karin kaso 5 akan kamfanonin Sadarwa

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya soke karin kaso 5 akan kamfanonin Sadarwa da ake shirin yi. Shugaban hukumar NCC, Aminu Maida ne ya bayyana hakan a yayin zantawa da manema labarai. Yace karin harajin kaso 5 akan kamfanonin sadarwar yana kunshene a cikin sabon kudirin dokar da majalisa ta amince dashi. Yace yana wajan aka kawowa shugaba Tinubu maganar karin amma yace ba zai kara saka 'yan Najeriya a cikin matsala ba. Yace a baya an dakatar da karinne amma yanzu an cireshi gaba daya.
Ina son shiga Aljannah>>Inji Shugaban kasar Amurka, Donald Trump

Ina son shiga Aljannah>>Inji Shugaban kasar Amurka, Donald Trump

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana son shiga Aljannah. Ya bayyana cewa dalili ma kenan da yake ta kokarin ganin ya kawo karshen yakin kasashen Russia da Ukraine. A baya Shugaba Trump ya gana da shugaban kasar Russia, Vladimir Putin sannan ya gana da shugaban kasar Ukràìnè sa shuwagabannin kasashen Turai. A nan gaba yace zai hada Putin da Zelenskyy su yi zaman sulhu. Tun kamin ya zama shugaban kasa yayi Alkawarin cewa idan ya ci zabe, zai tabbatar ya kawo karshen yakin.
Hukumar Shirya fina-finai ta Najeriya ta yi martani yayin da ake rade-radin Ali Nuhu ya rigamu gidan gaskiya

Hukumar Shirya fina-finai ta Najeriya ta yi martani yayin da ake rade-radin Ali Nuhu ya rigamu gidan gaskiya

Duk Labarai
Hukumar shirya fina-finai ta kasa, NFC ta musanta Bidiyon dake yawo a kafafen sadarwa dake ikirarin cewa, shugabanta, Ali Nuhu ya mutu. Jaridar Leadership tace NFC ta gaya mata cewa wannan rashin kyautawa ne da kuma abin Allah wadai inda hukumar ta nemi gwamnati ta saka ido akan kafafen sadarwa da kula da gudanarwarsu. Daraktan yada labarai na hukumar, Brian Etuk ya bayyana cewa, Ali Nuhu na nan lafiyarsa qalau. Yace kuma suna nan suna shirin daukar matakin da ya dace kan lamarin.
Fadar shugaban ƙasa ta yaba da ƙwazon Ribadu a matsayin NSA a watanni 25 da fara aiki

Fadar shugaban ƙasa ta yaba da ƙwazon Ribadu a matsayin NSA a watanni 25 da fara aiki

Duk Labarai
Fadar shugaban ƙasa ta yaba da ƙwazon Ribadu a matsayin NSA a watanni 25 da fara aiki Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa watanni 25 da Malam Nuhu Ribadu ya kwashe a matsayin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) sun zama juyin juya hali a yaki da ta’addanci, ’yan fashi da makami da sauran barazanar tsaro. Mataimakin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ya ce nadin Ribadu ya samar da sakamako a fili, ciki har da cafke manyan masu hannu a hare-haren ta’addanci, rage yawaitar hare-haren ’yan fashi a Arewa maso Yamma, ƙaruwar man fetur da ake samarwa ƙasa da miliyan ɗaya zuwa kusan miliyan 1.8 a kowace rana, da kuma rage rikicin ƙabilanci a wasu jihohi. Haka kuma, ya ce Ribadu ya taka muhimmiyar rawa wajen raunana kungiyar IPOB/ESN...
Labari Me Dadi: Shugaba Tinubu ya sa a rage farashin wankin Koda daga Naira Dubu 50 zuwa Naira Dubu 12

Labari Me Dadi: Shugaba Tinubu ya sa a rage farashin wankin Koda daga Naira Dubu 50 zuwa Naira Dubu 12

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin rage farashin wankin Koda daga Naira dubu 50 zuwa Naira Dubu 12. Wannan ragin farashin tuni ya fara aiki a Asibitocin gwamnati dake fadin Najeriya. Me magana da yawun shugaban kasar, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X. Yace shugaban yayi wannan ragi ne dan saukakawa masu ciwon koda. Wasu daga cikin Asibitocin gwamnatin tarayya da suka fara aiwatar da wannan ragi sun hada da Medical Centre (FMC), Ebute-Metta, Lagos; Federal Medical Centre (FMC), Jabi, Abuja; University College Hospital (UCH), Ibadan; da Federal Medical Centre (FMC), Owerri. Sauran sune University of Maiduguri Teaching Hospital (UMTH), Maiduguri; the Federal Medical Centre (FMC), Abeokuta;...
Sheikh Gumi ya gargadi Shugaba Tinubu inda ya fallasa wani shiri na yunkurin aika malamai Lahira

Sheikh Gumi ya gargadi Shugaba Tinubu inda ya fallasa wani shiri na yunkurin aika malamai Lahira

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya fallasa cewa akwai jami'an leken Asiri na kasar Israel, watau mossad a Najeriya. Ya kuma yi zargin cewa, akwai yiyuwar kisan Malamai a shigowar Mossad Najeriya. Malam ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta inda yace barin Mossad su samu karfi a Najeriya ba alheri bane. Sheikh Gumi ya bayar da misali da mutuwar tsohon shugaban kasa, General Sani Abacha inda yace akwai zargi mutuwarsa, domin ya mutu ne jim kadan bayan ganawa da yasir Arafat tsohon shugaban Falasdinawa. Gumi yace duk wanda ya baiwa shugaban kasar shawarar hada kai da kasar Israela bai bashi shawara me kyau ba. Ya ce ta yaya ma kasa Irin Israyla me kisan kiyashi za'a bada daa ta shigo Najeriya?
Gwamnatin tarayya tace zata rama tsaurara Yin Bizar da kasar Amurka ta kakabawa ‘yan Najeriya

Gwamnatin tarayya tace zata rama tsaurara Yin Bizar da kasar Amurka ta kakabawa ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin kasar Amurka tace duk dan Najeriyar dake neman Visa ta shiga kasarta dolene ya nuna yanda yake amfani da kafafen sadarwa na tsawon shekaru 5 baya. Dokar tace kin yin hakan zai iya sa a hana mutum Visar shiga kasar Amurkar. Saidai cikin gaggawa, Gwamnatin taraya ta sha Alwashin daukar irin wannan mataki akan 'yan kasar Amurka masu shigowa Najeriya. Kasar Amurka ta bayyana wannan sabuwar dokane ta kafar X wanda tace hakan na daga cikin shirin shugaban kasarta, Donald Trump na ganin ya samarwa kasar tasa tsaro. Me magana da yawun ma'aikatar tsaro ta Najeriya, Kimiebi Ebienfa ya bayyana cewa, Gwamnatin kasar Amurka tuni ta sanar dasu wannan shiri. Yace itama Najeriya zata dauki irin wannan mataki akan 'yan kasar Amurka masu neman Visa a Najeriya.