Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, ba lallai ya shiga Aljannah ba.
Ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai inda yace ya kyautatawa mutane amma baya tunanin Shiga Aljannah.
'Yar Najeriya, Tsohuwar Tauraruwar BBNAIJA, Natacha Akide wadda aka fi sani da Tacha ta yiwa mutane 145 kwalliya a cikin awanni 24 dan ta shiga kundin tarihin Duniya.
Ta aikata hakanne a Legas inda aka dauke ta Bidiyon yayin da take aikata hakan.
Duk da cewa an samu matsalar daukewar wuta amma tasha ta kammala wannan abu nata Lafiya.
Fadar shugaban kasa, ta tabbatar da cewa, ministan Kudi, Wale Edun Bashi da lafiya
Wata majiya daga fadar ta tabbatar wa da gidan jaridar Punchng hakan inda tace rashin lafiyar ta matsa masa.
Saidai tace ba Shanyewar rabin jiki bane sannan ba'a fitar dashi zuwa kasar waje ba, sannan shugaban kasa Bola Tinubu bai fara neman wanda zai maye gurbinsa ba.
Rahotanni sun ce Likitocin Najeriya ne ke kula da Ministan amma idan lamarin yayi kamari za'a iya fita dashi kasar waje.
Wani matashi daga jihar Katsina wanda yace ya fito ne daga garin Radda na jihar katsina kuma da uwane a wajan gwamnan Katsina watau Dikko Raddah ya koma Kirista.
Matashin wanda yace sunansa Abdullahi yace ya koma Kirista ne a Makaranta bayan da ya fara karanta Baibul ya kuma fahimceshi.
Matashin yace da ya gayawa mahaifiyarsa ta dauki abin da wasa amma daga baya da aka ga da gaske yake, an kamashi an daure tsawon watanni indaa yace amma duk da haka bai koma musulmi ba.
https://www.tiktok.com/@chizo_1_germany/video/7559944553420295446?_t=ZS-90VjSzhe8RM&_r=1
Dan Tiktok me wasan Barkwanci, Auwal ya musuluntar da wadda suke wasan Barkwanci tare me suna Christy ta koma musulma inda ta zabi sunan Fatima.
A Bidiyon da ya wallafa, an ganshi inda suka je masallaci tare da ita.
Sannan itama ta tabbatar da cewa, da gaskene ta karbi Addinin Musulunci.
https://www.tiktok.com/@auwal.44/video/7559721807893368082?_t=ZS-90ViIEMEJ0L&_r=1
Malamin Addinin Islama, Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana cewa, yana mamakin kalaman da Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau yayi da yace suna tare da Malam Lawal Triumph.
Malam Maqari ya bayyana cewa, abinda ya bashi mamaki shine shin wai akan me Izala take tare da Malam Lawal Triumph akan kalaman batancin da yawa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ko mene?.
Malam ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya dauki hankula sosai inda yake cewa Ibn Taimiyya yace girmama Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da kambamashi shine ke nuna tsayuwar Addini.
https://www.tiktok.com/@hassan.a.hassan.2/video/7559949237786512652?_t=ZS-90VfCQzDGTY&_r=1
Rahotanni sun ce tuni shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara neman wanda zai maye ministan Kudi, Wale Edun dashi.
Ministan Kudi, Wale Edun ya kwanta rashin lafiya bagtatan inda rahotanni suka ce shanyewar rabin jiki ce ta kamashi.
Rahotannin sun ce an garzaya dashi zuwa kasar waje.
Hakanan rahotannin sun ce ko da ya warke da wuya ya iya komawa bakin aikinsa.
Wannan ne yasa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara meman wanda zai maye gurbinsa dashi.
Rahotanni sun ce Shugaba Tinubu ya baiwa Gwamnan Babban bankin Najeriya, CBN umarnin maye gurbin Ministan kudin a wai taro da za'a yi a kasashen waje.
Wasu sabbin Hotunan Tauraruwar fina-finan Hausa, Momi Gombe sun dauki hankula sosai kuma sun jawo cece-kuce.
An ga Momi Gombe a Bidiyon sanye da doguwar riga tana ta rausaya.
Saidai wasu hankalinsu ya kai kan irin shigar da ta yi inda suke cewa ta nuna Rufaida da yawa.
Kalli Bidiyon anan
Wata matar aure a Arewa ta yi yaji saboda tace mijinta yana cutar da ita saboda 'ya'yansu 2 amma sai ya rika bata kudin cefanane
Tace yana ajiye kayan abinci kamar buhun shinkafa da man girki, amma sai ya bata Naira 100,000 wanda baya isanta yon cefane.
Akan hakane suka yi fada ta tafi gidansu.
https://twitter.com/_hafsat_paki/status/1977371222385029269?t=NsYHM3ZBZ_rvBAvum_wEbQ&s=19
Kelvin Oniarah Ezigbe dan shekaru 44 na daga cikin mutanen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa afuwa.
Shugaban wasu gungun 'yan fashine dake garkuwa da mutane
An zargeshi da hannu a kisan Sojoji da 'yansanda da dama.
An yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari saidai saboda nuna nadama da yayi, an rage shekarun zuwa 13.