Ni da kaina na je ofishin EFCC ba kama ni akai ba>> Inji Tsohon Me kula da kudi na kamfanin mai na kasa, NNPCL, Umar Ajiya Isa da ake zargi da satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man fetur din Najeriya
Tsohon Babban Jami’in Kudi (CFO) na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Umar Ajiya Isa, ya karyata rahotannin da ke cewa jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kama shi a ranar Litinin bisa zargin almundahana.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ajiya ya bayyana cewa, akasin yadda ake yadawa, shi da kansa ne ya je ofishin EFCC domin amsa tambayoyi, ba tare da an kama shi ba dangane da zargin handame cinikin man fetur har ma dala biliyan $7.2 a matatun mai na Warri da Port Harcourt.
“Ba wanda ya kama ni kan zargin batan wata dala biliyan $7.2 a matatar mai. Na je ofishin EFCC ne da kaina domin amsa tambayoyi sannan na koma gida. Na ji takaici ganin rahotanni a kafafen yada labarai da ke cewa an kama ni bisa zargin damfara,” in ji shi.
“Na yi aiki a...








