Gwamna Uba Sani Ba Abokina Ba Ne, Yarona Ne A Siyasa, Cewar Elrufa'i.
Wannan kalamai na El-Rufai na zuwane bayan da 'yan daba suka tarwatsa taron jam'iyyar su ta ADC a Jihar.
El-Rufai dai ya zargi Uba sani da cewa shine ya tura musu 'yan daba.
An ga yanda 'yan daba ke zuwa suna gaisuwar Habu Dan Damisa a Kaduna suna faduwa kasa suna kirari da zagezage.
Hakan yasa wasu fadin cewa, da alama har yanzu tsugune bata kare ba.
https://www.tiktok.com/@kabiruabdulsalamy6/video/7544733132801527058?_t=ZS-8zLeGCoTTeb&_r=1
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahya Kenan a wannan Bidiyon nata da aka ganta a wajan wani biki.
Bidiyon dai ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa shigar tata bata dace ba
https://www.tiktok.com/@mistinbestiebackup/video/7544876237164924168?_t=ZS-8zLd5QUaC6j&_r=1
Tsohon gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa yayi iya lissafinsa bai ga ta yanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sake con zabe ba a 2027.
Ya bayyana hakane hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace Tinubu na 3 zaizo a zaben.
Yace amma akwai yiyuwar za'a yi saben zagaye na biyu dan da wuya a samu wanda yayi nasara a zagayen farko.
Yaron dan Damisa, dan daba na Kaduna daya addabi mutane ya sake fitar da Bidiyo a karo na biyu inda yake cewa ya ga ana ta buga labarinsa.
Ya nanata gargadinsa inda yace zasu yi maganin masu murna da mutuwar me gidansu.
https://www.tiktok.com/@abdulrahamanaliyukafita/video/7544690317098847493?_t=ZS-8zLaaQjtnl3&_r=1
Jam'iyyar APC ta lashe ƙananan hukumomi 20 cikin 23 a zaɓen ƙananan hukumomi jihar Rivers da aka gudanar a jiya Asabar.
A ɗaya ɓangaren kuma, jam'iyyar PDP mai mulki a jihar, ta samu nasarar lashe ƙananan hukumomi uku, kamar yadda hukumar zaɓen jihar ta sanar.
Dakataccen gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya sha kaye a ƙaramar hukumarsa ta Opobo-Nkoro, inda ɗan takarar jam'iyyar APC ya lashe zaɓen.
Shugaban hukumar zaɓen, Dr Michael Odey ne ya sanar da sakamakon zaɓen a hedkwatar hukumar da ke titin Aba a Fatakwal kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta ruwaito.
A bara dai an yi wani zaɓen, inda Fubara ya tsayar da na hannun damarsa a jam'iyyar APP, inda suka doke ƴan takarar Wike a zaɓen, amma mutanen tsohon gwamnan suka je kotu, inda aka yi ta tafka shari'a har k...
Malami me wa'azi a Tiktok, Dr. Hussain ya bayyana cewa, abinda wasu 'yan darija suke yi na "Shirka" yafi abinda dan daba, Habu Dan Damisa da aka kashe a Kaduna na kisan mutane ba gaira babu dalili.
Malamin ace karkari dai ace habu yayi shaye-shaye ko kisa da sauransu, yace to hakan bai kai shirka ba a wajan Allah.
Sannan malamin yace Dabbaci da jahilci ne murna da mutuwar Dan Damisa, Addu'a ya kamata a yi masa.
https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7544116373421690168?_t=ZS-8zKrppT3L0a&_r=1
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ya shirya zuwa Kasa me tsarki dan tsinewa Azzalumai.
Ya bayyana hakane a Bidiyon jawabinsa biyo bayan harin da 'yan daba suka kai suka tarwatsa taronsu na jam'iyyar ADC ranar Asabar.
El-Rufai ya bayyana cewa, ya tsinewa wadanda suka aikata wannan abu.
https://www.tiktok.com/@mohammed.adamu69/video/7544467195057786130?_t=ZS-8zKqoveRqTZ&_r=1