Hanya ta hada tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da gwamna me ci, Abba Kabir Yusuf, da aka fi sani da Abba Gida-Gida.
Bayan haduwarsu, an ga yanda suka gaisa cikin Raha.
Kalli Bidiyon anan
Wani dan majalisar kasar Amurka, Bill Huizenga ya bayyana cewa, Shugaban kasarsu, Donald Trump da wuya ya kawowa Najeriya hari.
Yace maganar da Trump yayi, ya yi tane cikin bacin rai da damuwar asarar rayukan da ake yi a Najeriya.
Yace amma Trump takunkumi ne zai kakabawa kasar da masu mulkarta wanda hakan zai fi kawo hari amfani.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV.
Yace Trump ba mutum ne me son tashin hankali ba saboda a baya ya baiwa sulhu da zaman lafiya muhimmanci fiye da tashin hankali dan haka ba zai kawo Hari Najeriya ba.
Tsohon Shugaban sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, zagin da Ministan Abuja, Nyesom Wike yawa matashin soja da ya hanashi shiga wani Fili dan ya rusashi cin fuskane.
Buratai yace dolene a rika girmamawa da kuma sanya jami'an soji a gaba a kasarnan.
Yace tsaro shine ke zuwa farko kuma zagin da Wike yawa matashin sojan cin fuskane da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sojan da hukumar sojojin Najeriya.
Buratai yace dolene Wike ya fito ya baiwa matashin sojan hakuri, da shugaba Tinubu, dama Hukumar soji.
Yayi kira ga shugaba Tinubu da ya dauki matakin da ya dace akan lamarin.
Wike dai ya zagi wani matashin soja ne da ya hanashi shiga wani fili wanda na sojoji ne dan hana ci gaba da gini a filin, sojan yace an bashi umarnine.
Dan majalisar wakilai Hon. Isa Mohammed Anka wanda shine shugaban Kwamitin majalisar wakilai dake kula da iyakokin Najeriya ya koka da cewa akwai hanyoyin Shigowa Najeriya daga kasashen waje guda 1,978 amma guda 84 ne kadai jami'an tsaro ke kula dasu.
Ya bayyana hakane ranar Talata a Abuja wajan kaddamar da kwamitin na wucin gadi.
Ya kara da cewa, wannan matsalar itace tasa ake samun yawan safarar mutane da miyagun kwayoyi da makamai da sauran abubuwan laifi.
Yace abinda yasa Gwamnati bata iya samar da tsaro sosai a wadannan hanyoyin shigowa Najeriya sun hada da karancin kudi, da sarkakkiyar hanyoyin da karancin ma'aikata.
Ya jinjinawa jami'an Kwastam, dana Immigration wajan kokarin da suke na kare Najeriya akan iyakoki inda yace akwai bukatar hadin kan sauran jami'an tsaron N...
Bankin Duniya ya fitar da rahoto kan yanda ake raba tallafin rage radadin Talauci ga talakawa.
Bankin yace kaso 44 cikin 100 ne kacal na mutanen da aka ce ana baiwa tallafin ke samun sa.
Bankin yace kuma ko abincin da ake ciyar da dalibai ya kamata a karashi.
Hakan na zuwane bayan da ministan kudi Wale Edun yace sun raba naira 25,000 ga mutane Miliyan 8.5 inda ya kara da cewa akwai sauran mutane Miliyan 6.5 da zasu biya nan da karshen shekara.
Bankin Ya nuna damuwa kan yanda Najeriya ke kasancewa tana dogaro da kasashen waje wajan samun kudin da zata tallafawa Talakawanta.
Sojan Ruwan Najeriya, Lieutenant A.M. Yerima na shan yabo bayan Tirka-Tirkar da suka yi da ministan Abuja, Nyesom Wike kan sai ya shiga wajan wani gini ya hana amma sojan ya hanashi shiga.
Wike ya kira har shugaban tsaro gaba daya na kasa amma Sojan yawa Shugaban bayanin cewa na sama dashi ne ya sashi wannan aiki.
Saidai Wike ya koma yana zagin sojan da cewa, wawa ne amma sojan yace shi ba wawa bane.
Wani daga cikin yaran Wike ya gayawa sojan cewa ba zaka yi shiru ba oga na magana kana magana, Shina Wike din yace masa yayi Shiru amma yace ba zai yi shiru ba.
Lamarin ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta inda da dama suka yabawa sojan.
Saidai wasu daga cikin yaran Wike sunce sojan ya sabawa ka'idar aiki inda suke cewa hakan daidai yake da yunkurin yin juyin mulki.
...
Tauraron fina-finan Hausa, KB International ya fito yayi magana bayan da Bidiyonsa ya bayyana aka ga yana cewa zai iya yin tallar Giya akan Naira Miliyan 50.
KB a Bidiyon jawabinsa yace datse Bidiyon aka yi inda yace suna maganane kuma wasa ake.
Ga cikakken bayaninsa kamar haka:
https://www.tiktok.com/@kb_international/video/7571074899826035976?_t=ZS-91JcALCMqkj&_r=1
Tauraron da kwallon kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa, wasan cin kofin kwallon kafa na Duniya na shekarar 2026 shine na karshe da zai buga.
Ronaldo ya bayyana hakane a waa hira da aka yi dashi daga kasar Saudiyya a wajan wani taro na yawon bude ido da zuba hannun Jari.
Hakanan Ronaldo ya sanar da cewa, nan da shekaru 2 zai daina buga kwallonnkafa.
A dasu da safene aka ga Bidiyon Alhassan Ado Doguwa yana kwambo a kan titin Birnin Landan na kasar Ingila.
Lamarin ya jawo cece-kuce inda mutane sukai ta mamakin dan majalisar Tarayya guda da nuna irin wannan halayya.
Saidai ashe kallo be kare ba, a karo na biyu an ga Doguwa yana daukar hoton a cikin dakin Otal dib da ya sauka inda a wannan karin har abinci yaci a cikin bandaki.
https://twitter.com/Asad_Mukty/status/1988160598086164882?t=k_sh_5vZZm33_Yz-mo4w3Q&s=19