Monday, May 11
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: Rahama Saidu me babban Shago inda ta mikawa namiji da yaje sayayya hannu su gaisa amma yaki yadda ya bata hannu

Kalli Bidiyon: Rahama Saidu me babban Shago inda ta mikawa namiji da yaje sayayya hannu su gaisa amma yaki yadda ya bata hannu

Duk Labarai
Rahama Saidu me babban shago ta dauki hankula inda ta mikawa daya daga cikin kwatomominta hannu su gaisa amma yaki yadda ya mika mata hannu. Inda a gefe daya kuma ta mikawa Soja Boy hannu suka gaisa. Lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa wai Namiji ne yake kin shan hannun mace amma ita tana mika masa hannu. A baya dai Soja Boy da Rahama Saidu sun gaisa hakanan ya ma rungumeta lamarin da ya jawo cece-kuce me zafi. https://www.tiktok.com/@abu_ayrin_backup/video/7553946644190989575?_t=ZS-9029A5Isqh7&_r=1
Babu kasar data kai Najeriya dadi, kada ku je ku ki dawowa, Shugaba Tinubu ya gayawa Kiristoci masu shirin tafiya Jerusalem dan aikin ibada

Babu kasar data kai Najeriya dadi, kada ku je ku ki dawowa, Shugaba Tinubu ya gayawa Kiristoci masu shirin tafiya Jerusalem dan aikin ibada

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gargadi kiristoci masu son tafiya jeru salem Ibada cewa kada wanda ya makale a can yaki dawowa Najeriya. Shugaban yace babu kasar data kai Najeriya 'yanci da dadi musamman idan mutum na zaune a wata kasar ba bisa ka'ida ba. Shugaban ya bayyana hakane ta bakin Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume a yayin da kiristocin ke shirin tafiya aikin ibadar.
Karya ake min ban ce zan baiwa Yarbawa fifiko ba idan na zama shugaban kasa>>Atiku Abubakar

Karya ake min ban ce zan baiwa Yarbawa fifiko ba idan na zama shugaban kasa>>Atiku Abubakar

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, ba gaskiya bane labarin da yake yawo cewa wai yace zai baiwa yarbawa kulawa da mukamai na musamman idan ya zama shugaban kasa. Atiku yace wanda ya fitar da sanarwar da yawunsa me suna Kola Johnson be sanshi ba. Atiku ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa Paul Ibe. Inda ya bukaci a yi watsi da wannan magana.
Kalli Bidiyon: Duk da cewa kudin Tarihin Duniya yace ba ruwansa da shiriritarta, Matashiyarnan mara Kunya ‘yar Legas tace ba zata fasa ba, sai ta yi Alfasha da maza 100

Kalli Bidiyon: Duk da cewa kudin Tarihin Duniya yace ba ruwansa da shiriritarta, Matashiyarnan mara Kunya ‘yar Legas tace ba zata fasa ba, sai ta yi Alfasha da maza 100

Duk Labarai
Matashiyar nan marar kunya ta jihar Legas, Ayomiposi Oluwadahunsi wadda aka fi sani da Mandy Kiss tace duk da kundin tarihin Duniya yace ba zai karrama ta ba idan ta yi lalata da maza 100, ba zata fasa ba. Tace tuni ta sayi fakiti na kwandam inda take gayyatar maza zuwa Ikorodu. Tace ko da mutum ba zai yi ba, tana gayyatarsa ya je ya sha kallo. Ta bayyana cewa dai a watan Oktoba ne zata aikata wannan masha'a saidai bata fadi sunan wajan da zata aikata hakan ba. https://twitter.com/Teeniiola/status/1970723550521893060?t=_QdTAUIMpixvtqGHkHOeLA&s=19 https://twitter.com/Teeniiola/status/1971143834601132165?t=1bukeNydE-hM6KU_yjWQ1g&s=19
Duk da rage farashin man fetur da Dangote yayi, gidajen mai har yanzu suna sayarwa a tsohon farashi me tsada

Duk da rage farashin man fetur da Dangote yayi, gidajen mai har yanzu suna sayarwa a tsohon farashi me tsada

Duk Labarai
Rahotanni sun ce har yanzu gidajen man fetur na sayar da man a farashi me tsada duk da rage farashin da matatar man fetur ta Dangote ta yi. A makon daya gabata ne Matatar man ta sanar da rage farashin daga Naita 865 zuwa naira 820 akan kowace lita musamman tace saboda tankokin man ta 1000 zasu fara jigilar man zuwa gidajen mai kyauta. Saidai binciken da jaridar Punchng ta yi yace har yanzu a jihohin Legas da Ogun da sauran wasu jihohi gidajen man basu fara sayar da man a sabon farashi ba.