Wednesday, March 4
Shadow

Duk Labarai

Gwamnatin Amurka zata fara bukatar ‘yan Najeriya dake son zuwa kasar su ajiye dala $15,000(Naira Miliyan Asihirin da biyu) idan mutum ya dawo gida za’a mayar masa da kudinsa, idan kuma ya ki dawowa za’a rike kudin

Gwamnatin Amurka zata fara bukatar ‘yan Najeriya dake son zuwa kasar su ajiye dala $15,000(Naira Miliyan Asihirin da biyu) idan mutum ya dawo gida za’a mayar masa da kudinsa, idan kuma ya ki dawowa za’a rike kudin

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Amurka na shirin kakabawa kasashen Duniya sabuwar doka ta shiga kasarta. Kasashen da wannan sabuwar dokar zata shafa sune kasashen da basu da cikakkun bayanai na 'yan kasarsu da kuma wadanda 'yan kasarsu ke yawan zuwa Amurka basa komawa kasashen su na haihuwa. Yawanci wadanda abin zai shafa sune masu zuwa Amurka dan yawon shakatawa ko kasuwanci. Dokar tace za'a bukaci mutane su rika ajiye dala $15,000, kwatankwacin Naira Miliyan 22 kenan, idan sun je Amurka sun ki dawowa gida Najeriya ko kasashensu na Asali, za'a rike kudin, amma idan sun dawo gida, za'a mayar musu da kudadensu. Badai a bayyana sunayen kasashen da lamarin zai shafa ba amma masu sharhi akan al'amuran yau da kullun sun yi ittifakin akwai 'yan Najeriya a ciki.
Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan N26.38bn wajan kula da jiragen samansa a cikin watanni 18

Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan N26.38bn wajan kula da jiragen samansa a cikin watanni 18

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta kashe akalla Naira Biliyan N26.38bn wajan kula da jiragen saman shugaban kasar a cikin watanni 18 da suka gabata. Hakan na kunshene a cikin rahoton da kungiyar, Govspend ta fitar wadda ke saka ido akan yanda gwamnati ke kashe kudaden Talakawa. Rahoton yace an kashe wadannan kudadenne a tsakanin July 2023 zuwa December 2024. Hakanan rahoton yace shima tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kashe Naira Biliyan N81.80bn wajan kula da jiragen saman sa a tsakanin shakerar 2016 zuwa 2022.
Kaine Zabin Kanawa a 2027, Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta baiwa shugaba Tinubu tabbaci

Kaine Zabin Kanawa a 2027, Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta baiwa shugaba Tinubu tabbaci

Duk Labarai
Jam'iyyar APC Reshen jihar Kano ta baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tabbacin goyon baya a zaben shekarar 2027 me zuwa. Jam'iyyar ta kuma bayyana Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar a jihar. Sun bayyana hakane yayin wani zama da aka yi a gidan tsohon shugaban jam'iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Shugaban jam'iyyar a jihar, Alhaji Abdullahi Abbas ya bayyana cewa, an shirya taronne dan warware matsalolin cikin gida na jam'iyyar da kuma shiryawa babban zaben shekarar 2027 dake tafe.
Kalli Bidiyon: Ba yaran nan kadai, har iyayensu ya kamata Shugaba Tinubu ya karramasu>>Inji Sheikh Gadon Kaya

Kalli Bidiyon: Ba yaran nan kadai, har iyayensu ya kamata Shugaba Tinubu ya karramasu>>Inji Sheikh Gadon Kaya

Duk Labarai
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Abdallah Gadon kaya yayi kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya karrama yara mata da suka yi nasarar lashe gasar Turanci ta Duniya tare da iyayensu. Yace ya kamata a karrama hadda iyayensu saboda yanda suka kula dasu suka basu tarbiyya da ilimi da har suka kai wannan mataki. Malam yace ba 'yan kwallo kadai shugaban kasar zai rika karramawa ba. inda yace shugaban zai bar mummunan tarihi idan bai karrama wadannan yara ba. https://www.tiktok.com/@abdul_prince_/video/7535249986481622328?_t=ZS-8ye0ppEjQ37&_r=1 Wannan kira na malam na zuwane bayan na Sheikh Isa Ali Pantami na cewa ya kamata shugaba Tinubu yawa yaran irin karramawar da yawa 'yan Kwallon Najeriya.
Da Duminsa: Gwamnati ta fitar da gargadin Ambaliyar ruwan da za’a kwashe kwanaki 5 ana yi a jihohi 19, karanta jadawalin Jihohin

Da Duminsa: Gwamnati ta fitar da gargadin Ambaliyar ruwan da za’a kwashe kwanaki 5 ana yi a jihohi 19, karanta jadawalin Jihohin

Duk Labarai
Gwamnati tacw za'a kwashe kwanaki 5 ana ruwan sama a jere wanda hakan zai iya jawo ambaliyar ruwa a jihohi 19 da furare 76. Bangaren kula da ambaliyar ruwa na ma'aikatar Muhalli ne ya fitar da wannan sanarwar. Hakan na zuwane yayin da ambaliyar ruwan tuni ta shiga jihohin Gombe, Plateau, Ogun, Anambra, Delta, da Legas a ranar Talata. Wannan ambaliyar ruwa a cewar sanarwar zata fara ne daga ranar 5 zuwa 9 ga watan Augusta. Garuruwan da lamarin zai shafa sun hada da Akwa-Ibom (Edor, Eket, Ikom, Oron, Upenekang); Bauchi (Tafawa-Balewa, Azare, Jama’are, Kari, Misau, Jama’a); Ebonyi (Abakaliki, Echara, Ezilo); Cross-River (Ogoja Edor, Obubra); Nasarawa (Keana, Keffi, Wamba); Benue (Agaku, Buruku, Gboko, Igumale, Ito, Katsina-Ala, Ugba, Vande-Ikya); Kaduna (Jaji, Kafancha, Birnin-Gwa...
A wane littafin aka ce sai an sha wuya a gidan aure? Maza ku ji tsoron Allah sai ku auri mace tubarkallah amma bayan wata 7 ta rame ta lalace>> Inji Nafisa Ishak

A wane littafin aka ce sai an sha wuya a gidan aure? Maza ku ji tsoron Allah sai ku auri mace tubarkallah amma bayan wata 7 ta rame ta lalace>> Inji Nafisa Ishak

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Nafisa Ishak ta bayyana damuwa game da yanda wasu maza ke wa matan da suka aura rikon sakainar kashi. Ta bayar da misali da kanta cewa tana gidan miji duk ta lalace amma data fito sai da ta ci sama da Tiriliyan 3 kamin ta zama yanda ake kallonta. Ta yi kira ga maza da su ji tsoron Allah akan yanda suke rikon mata. Wadannan kalamai nata sun jawo cece-kuce sosai. https://www.tiktok.com/@nafisa_ishak/video/7533924472827415864?_t=ZS-8ydvIyOE6l6&_r=1
Dan majalisar tarayya daga jihar Zamfara Kabiru Mai Palace ya gyara makabartu 80 a matsayin aikin da yawa mazabarsa

Dan majalisar tarayya daga jihar Zamfara Kabiru Mai Palace ya gyara makabartu 80 a matsayin aikin da yawa mazabarsa

Duk Labarai
Dan majalisar tarayya daga Zamfara Kabiru Mai Palace ya gayara makabartu 80 a jihar. Da yake magana da manema labarai ranar Talata wajan kaddamar da aikin, yace kowane mutum idan ya rasu makabarta za'a kai a binneshi. Makabartun da aka gyara na tsakanin kananan Hukumomin Tsafe da Gusau ne Ya kuma bayyana cewa gyaran ya zama dole lura da halin lalacewa da makabartun suke. Ya sha Alwashin daukar masu gadin makabartar da kuma biyansu Haraji.