Wednesday, March 4
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo: Yanda aka daina sakani a Fim saboda bana bada hadin kai ayi…. dani>>Inji jarumar fina-finan Hausa, Ummi Hutu

Kalli Bidiyo: Yanda aka daina sakani a Fim saboda bana bada hadin kai ayi…. dani>>Inji jarumar fina-finan Hausa, Ummi Hutu

Duk Labarai
Tauraruwar Fina-finan Hausa dake a Kaduna, Ummi Hutu ta yi korafin cewa, an daina sakata a fim saboda bata bada hadin kai. Ta bayyana hakane a wani Bidiyon ta daya bayyana a Tiktok. Tace Amma ta samu wata harkar shine ake mata bita da kulli ana mata bakin ciki amma tace masu yi basu isa ba. https://www.tiktok.com/@iya_habu/video/7535086847328914694?_t=ZS-8ydKY609Agr&_r=1
Kalli Bidiyo: Babban Burina shine in zama Sanata, Zan Fito takara kuma babu wanda ya isa yasa in janye>>Inji Sheikh Salihu Zaria

Kalli Bidiyo: Babban Burina shine in zama Sanata, Zan Fito takara kuma babu wanda ya isa yasa in janye>>Inji Sheikh Salihu Zaria

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Salihu Zaria ya bayyana cewa yana da sha'awar zama sanata. Yace ba zasu rika bari wadanda basu cancanta ba su ci gaba da mulkar mutane ba. Yace zai fito takarar sanata kuma babu wanda ya isa yasa ya janye. https://www.tiktok.com/@yunus.abu.bakr6/video/7534836390903745848?_t=ZS-8ydK7oiav8T&_r=1
Kalli Bidiyon: Na taba aure sau daya amma yanzu bani da aure amma ina fatan in yi aure in haihu>>Inji Ladidi

Kalli Bidiyon: Na taba aure sau daya amma yanzu bani da aure amma ina fatan in yi aure in haihu>>Inji Ladidi

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Ladidi tubeless ta bayyana cewa, ta taba aure a baya amma auren ya mutu. Tace bata taba haihuwa ba amma tana fatan nan gaba ta sake yin aure ta haihu. Ladidi Tubeless ta bayyana hakane a hirar da BBCHausa suka yi da ita. https://www.tiktok.com/@ladidi_tubbles/video/7535082673556032824?_t=ZS-8ydI3fmSNjF&_r=1
Gwamnatin tarayya ta rabawa masu kananan sana’o’i tallafin Naira 250,000 dan karfafasu a Jihar Ondo

Gwamnatin tarayya ta rabawa masu kananan sana’o’i tallafin Naira 250,000 dan karfafasu a Jihar Ondo

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta rabawa masu kananan sana'o'i tallafin Naira 250,000 kyauta a jihar Ondo. Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya jagoranci rabon inda yace wannan tsari ne da ake yinshi a kowace sashe na kasarnan dan karfafa masu kananan sana'o'i. Yace wannan daya daga cikin tsare-tsaren shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne na kokarin karfafa kananan 'yan kasuwa da suka yi zarra. Yace kudin ba bashi bane, an bayar dasu ne dan gwamnati ta karfafa 'yab kasuwar kyauta.
Manufofin Tinubu sun ƙara jefa miliyoyin ƴan Najeriya cikin talauci – Falana

Manufofin Tinubu sun ƙara jefa miliyoyin ƴan Najeriya cikin talauci – Falana

Duk Labarai
Fitaccen lauyan nan a Najeriya mai kare haƙƙin bil adama, Femi Falana ya caccaki manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu inda ya ce "manufofin masu tsauri" sun shafe masu matsakaicin samu tare da ƙara jefa miliyoyin mutanen ƙasar cikin talauci. Falana ya ce duk da cewa a baya-bayan nan shugaban ƙasar ya fito ya bayyana cewa ya san irin halin ƙunci da ƴan Najeriya ke ciki, manufofinsa sun ƙara talauta al'umma. Lauyan mai muƙamin SAN ya shaida hakan ne a hirar da ya yi a gidan Talabijin na Channels inda kuma ya ga baiken yadda gwamnati ke cefanar da kamfanoni ga ƴan kasuwa lamarin da a cewarsa ya ci karo da ƙoƙarin da ake na magance bambancin samu a tsakanin ƴan Najeriya. Ya ƙara da cewa ya zama dole gwamnati ta sake nazari kan manufofinta tare da samar da tallafi ga ƴan Naje...
Da kasuwancina na habaka sosai, bankuna sun rika aikomin tsala-tsalan ‘yan mata dan in mayar da kudin ajiya ta can>>Inji Attajirin Najeriya, Femi Otedola

Da kasuwancina na habaka sosai, bankuna sun rika aikomin tsala-tsalan ‘yan mata dan in mayar da kudin ajiya ta can>>Inji Attajirin Najeriya, Femi Otedola

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Femi Otedola ya bayyana cewa a lokacin kasuwancinsa na habaka sosai, bankuna suna aika mata kyawawan 'yan mata dan su ja hankalinsa ya mayar da ajiyar kudi acan. Ya bayyana hakane a wani littafin tarihin rayuwarsa da yanda ya gudanar da kasuwanci da yake shirin wallafawa wanda jaridar TheCable tace ta samu gani. Yace ya samu matsala bayan da ya saro man fetur daga kasashen wajan lokacin man yana a farashin Dala $140 amma aka samu tsaiko be karaso Najeriya ba sai da ya koma farashin dala $40. Yace hakan ya jefashi cikin matsanancin bashi. Hakanan yace karya darajar Naira ma ya kara jefashi cikin wahala sosai. Yace a lokacin da bashin bankin ya mai yawa kuma sai bankin suka koma aika masa da jigba-jibgan mazaje masu fadin kirji dan su bashi tsoro ya biya.
Da Duminsa:Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sauka a Akure wajan taron tallafawa kananan masana’antu

Da Duminsa:Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sauka a Akure wajan taron tallafawa kananan masana’antu

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim shetty ya sauka a garin Akure jihar Ondo inda yake ziyarar aiki wajan taron kaddamar da tallafawa kananan masana'antu. Me magana da yawun Kashim Shettima, Stanley Nkwocha, ya tabbatar da hakan inda yace Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa dana Ekiti, Biodun Oyebanji da sauran manyan jami'an gwamnati ne suka tarbi Kashim Shettima a filin jirgin. An shirya taron ne dan tallafawa kananan masana'antu a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Kalli Bidiyon Barnar kudi: Yanda Titin Legas zuwa Calabar da Gwamnatin Tinubu ta kashe Naira Tiriliyan 15 akai ya fara lalacewa tun kamin a kammalashi

Kalli Bidiyon Barnar kudi: Yanda Titin Legas zuwa Calabar da Gwamnatin Tinubu ta kashe Naira Tiriliyan 15 akai ya fara lalacewa tun kamin a kammalashi

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana na titin Legas zuwa Calabar wanda Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Tiriliyan 15 akanshi wanda kuma ya fara lalacewa. Wanda ya dauki Bidiyon ya nuna yanda ba'a gina Makwararar ruwa a gefen titin ba wanda hakan ya fara kawo zaizayar kasa titin na lalacewa. https://twitter.com/omoelerinjare/status/1952502828662132988?t=_gFpF8_OVZli6WfLIam3cg&s=19
Kalli Bidiyo: Ku rufawa kanku Asiri kada ku shiga aikin Soja, Wani sojan Najeriya ya gargadi matasa

Kalli Bidiyo: Ku rufawa kanku Asiri kada ku shiga aikin Soja, Wani sojan Najeriya ya gargadi matasa

Duk Labarai
Wani sojan Najeriya ya gargadi matasa da cewa su rufawa kansu Asiri kada su shiga aikin soja. Yace aikin ba dadi kuma ba'a wa sojojin Adalci, domin kuwa suna bautawa kasarsu ne amma kasar bata damu dasu ba. Sojan ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1952421319493951945?t=TdaI_dOy4snO17Jp2gQBvQ&s=19
Sabon Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC inda shuwagabannin jam’iyyar na jihohi suka hada kai suka ce basu yadda da su Atiku da Peter Obi ba

Sabon Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC inda shuwagabannin jam’iyyar na jihohi suka hada kai suka ce basu yadda da su Atiku da Peter Obi ba

Duk Labarai
Shuwagabannin jam'iyyar ADC na jihohi sun hade kai inda suka ce basu yadda da shugabancin David Mark a matsayin shugaban rikon kwarya na jam'iyyar ba. Hakan na zuwane a wata sanarwa da shugaban kungiyar tasu me suna,Amb. Elias Adokwu ya sakawa hannu tare da sa hannun sakataren watsa labarai na kungiyar, Godwin Alaku. Sun bayyana cewa hadakar 'yan Adawa ta su Atiku karfa-Karfa ta musu. Sun ce kuma hakan ya sabawa dokokin jam'iyyar.