Monday, December 15
Shadow

Duk Labarai

Hukumar kula da birnin tarayya Abuja zata sake gina sabuwar Hukumar zabe me zaman kanta INEC, ‘yan Najeriya da yawa sun ce wata hanyar bata kudi ce

Hukumar kula da birnin tarayya Abuja zata sake gina sabuwar Hukumar zabe me zaman kanta INEC, ‘yan Najeriya da yawa sun ce wata hanyar bata kudi ce

Duk Labarai
Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, FCTA ta sanar da shirin sake gina sabuwar Hukumar zabe me zaman kanta, INEC. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zai kaddamar da fara ginin na INEC wanda na daga cikin bikin cikarsa shekara 2 akan mulki. Ba dai a bayyana ainahin nawaye kudin da za'a yi amfani dasu wajan sake gina sabuwar hukumar INEC din ba amma an ce zasu kai Biliyoyin Naira. Da aka binciki cewa, me yasa FCTA zata gina INEC saboda lura da INEC hukuma ce me zaman kanta, wata majiya daga hukumar ta FCTA tace ai sune suka gina hukumomi da yawa a Abuja hadda ma majalisar tarayya. Sannan sake ginin bashi da wata alaka da kokarin nuna iko da hukumar ta INEC.
Naira Biliyan N39bn d aka kashe wajan gyaran babban dakin taro na Abuja wanda aka sakawa sunan shugaban Tinubu, kudin zasu iya gina Asibitoci 312 da Ajujuwan makarantu 1,200

Naira Biliyan N39bn d aka kashe wajan gyaran babban dakin taro na Abuja wanda aka sakawa sunan shugaban Tinubu, kudin zasu iya gina Asibitoci 312 da Ajujuwan makarantu 1,200

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja ya gyara babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja wanda ya sakawa sunan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Lamarin ya jawo cece-kuce inda masu suka ke cewa, a zamanin tsohon shugaban kasa janar IBB ne aka gina dakin kuma sunansa ya kamata a saka. Saidai wani abu da ya kara daukar hankula shine maganar kudin da aka kashe wajan gyaran inda Ministan yace sun kashe Naira Biliyan 39 wajan yin wannan gyara. Masu bin diddigi sun ce Naira Biliyan 39 dinnan zata iya gina Asibitoci 312 da Ajujuwan Karatu 1,200. Hakan dai na nuna rashin muhimmanci da shuwagabanni basu baia bukatar talakawa, ko kuma ace rashin saka kudi inda aka fi bukatarsu.
An zargi cewa An fifota baiwa Adam A. Zango kulawa fiye da sauran wadanda suka yi Hadari tare a Asibiti inda aka bar su duk da sun fi shi jin jiki, har daya ta rasu daga ciki

An zargi cewa An fifota baiwa Adam A. Zango kulawa fiye da sauran wadanda suka yi Hadari tare a Asibiti inda aka bar su duk da sun fi shi jin jiki, har daya ta rasu daga ciki

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Bayan da kafar Hutudole ta wallafa labarin wata matashiya me suna Natasha wadda ta koka kan yanda mutane ke baiwa Adam A. Zango fifikon Addu'a fiye da sauran wadanda suka yi hadari tare, Wani da yayi ikirarin cewa yana asibitin da aka kai su Adam A. Zango me suna Ibrahim Kalil yace ko a Asibiti haka aka fi baiwa Adam A. Zango fifiko fiye da sauran wadanda suka yi hadarin tare. Ga abinda ya fada kamar haka: "Wallahi gaskiya ta faɗi ko a asibitin da aka kawo su ana zuwa kan Adam Za...
Yawan man fetur da Najeriya ke shigo dashi daga kasashen waje yayi kasa sosai irin wanda ba’a taba gani ba a cikin shekaru 8

Yawan man fetur da Najeriya ke shigo dashi daga kasashen waje yayi kasa sosai irin wanda ba’a taba gani ba a cikin shekaru 8

Duk Labarai
Yawan man fetur din da Najeriya ke shigo dashi daga kasashwn waje yayi kasa sosai ta yanda ba'a taba ganin hakan ba a cikin shekaru 8 da suka gabata. Wannan na da alaka da yanda matatar man fetur ta Dangote ke aiki tukuru wajan tace isashshen man fetur da kuma danne masu yunkurin shigo da man fetur din daga kasashen waje. Rahoton jaridar Bloomberg yace daga watan Janairu na shekarar 2025 zuwa 24 ga watan yawan man fetur din da ake shigowa dashi Najeriya ya bai wuce ganga 110,000 ba a kullun. Wannan shine mafi karancin man fetur da aka shigo dashi Najeriya daga kasashen waje idan aka kwatanta da ganga 200,000 da ake shigowa da ita kullun a shekarar 2017 inda wani lokacin har tana kaiwa ganga 400,000. Rahoton yace matatar Dangote wadda ke da karfin data fi kowace matatar man fetu...
Bidiyo: Babana Tare suka yi hadari da Adam A. Zango amma ba wanda ke maganarsa saikace Adam A. Zango ne kadai mutum>>Inji Wannan matashiyar

Bidiyo: Babana Tare suka yi hadari da Adam A. Zango amma ba wanda ke maganarsa saikace Adam A. Zango ne kadai mutum>>Inji Wannan matashiyar

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shiga Tasharmu ta WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g Wata matashiya me suna natasha ta fito tana sukar mutane da cewa tun bayan da tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango yayi hadari shi kadai ake magana akansa. Tace akwai sauran mutane da Adam. A. Zango yayi hadasu tare dasu wasu ma sun mutu. Tacw akwai babanta wanda suka yi Hadari tare da Adam A. Zango wanda tace yana can wajan kulawa ta musamman bai ma san halin da yake ciki ba. https://www...
Matan Yarbawa sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin samar masa da kuri’u Miliyan 1

Matan Yarbawa sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin samar masa da kuri’u Miliyan 1

Duk Labarai
Wata Kungiyar matan yarbawa a jihar Osun ta yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin kuri'u Miliyan 1 a zaben 2027. Kungiyar tace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zabinta a zaben 2027. Matan ta bakin wakiliyarsu a jihar Osun, Adesola Ayangbil sun bayyana cewa, sun fara yakin neman zabe ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gida'gida kamin zuwa zaben shekarar 2027. Sun bayyana hakane a ofishin yakin neman zaben Tinubu da Shettima. Sun ce sun yaba da shugabancin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekaru 2 da suka gabata.
Tinubu ya tseratar da Najeriya daga fadawa matsalar Talauci>>Inji Gwamnan Anambra

Tinubu ya tseratar da Najeriya daga fadawa matsalar Talauci>>Inji Gwamnan Anambra

Duk Labarai
Gwamnan jhar Anambra, Charles Soludo ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tseratar da Najeriya daga fadawa kangin Talauci. Ya bayyana hakane a cikin jawabinsa na ranar 'yanci inda yace tsare-tsaren tayar da komar tattalin arziki na gwamnatin shugaban kasar na aiki yanda ya kamata. Yace tattalin arzikin Najeriya a yanzu ya dauki saiti kuma za'a iya ganin tabbacin hakan ta hanyar yabo da shugaban kasar ke samu daga hukumomin Duniya irin su IMF da bankin Duniya da sauransu. Soludo yayi kira ga jam'iyyun Siyasa da su hada kai a muradi na bai daya na ci gaban kasa.
Ko makaho yasan ina aiki a kasarnan>>Shugaba Tinubu

Ko makaho yasan ina aiki a kasarnan>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Ko mahako yasa yana ayyukan ci gaba a Najeriya. Shugaban ya bayyana hakane yayin kaddamar da titin Apo-Wasa dake Abuja. Shugaban yace Najeriya haka take shekarun 1960 ko kuwa haka take a shekaru 3 da suka gabata? Amma 'yan Adawa babu me yabawa sai suka. Shugaban ya baiwa 'yan Adawa shawarar su mayar da hankali wajan gyara matsalarsu kamin zaben 2027 dan kada wani ya zargeshi da yin magudi. Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ne ya wakilci shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a wajan kaddamar da titin.
GA WANI DARASI DA YA FARU YAU: Wannan hoton wani iyali kenan da suka yi bankwana da kasar India da nufin za su je cika burinsu na komawa kasar Ingila da zama ashe ajali ke kiransu

GA WANI DARASI DA YA FARU YAU: Wannan hoton wani iyali kenan da suka yi bankwana da kasar India da nufin za su je cika burinsu na komawa kasar Ingila da zama ashe ajali ke kiransu

Duk Labarai
GA WANI DARASI DA YA FARU YAU: Wannan hoton wani iyali kenan da suka yi bankwana da kasar India da nufin za su je cika burinsu na komawa kasar Ingila da zama ashe ajali ke kiransu A Yau ta ruwaito bayanai sun nuna mijin mai suna Pratik Joshi kwarren mai masanin kwamfuta ne wanda ya dade yana mafarki kwashe iyalansa su koma Ingila da zama. Sannan matarsa sunan ta Dr. Komi Vyas wacce ta ajiye aikinta tayi bankwana da da su akan mafarkinta na komawa Ingaila da zama ya tabbata…. Kwatsam yau sun hau jirgin sama har suka yi wannan hoto suka tura wa dangi a matsayin bankwana sun bar kasa sai jirginsu kirar Air India Flight 171 ya yi hatsari kuma kusan duka fasinjoji fiye da 200 dake jirgin suka mutu Allah sarki rayuwa ashe duniyar ma za su bari! Allah ya jikan mamatanmu!
Ni Dai Ban San Inda Sauran ‘Yan Matan Fim Suka Samo Na Su GLK Din Ba, Amma Ni Tawa Baby Na Ne Ya Siya Min, Inji Samha M. Inuwa

Ni Dai Ban San Inda Sauran ‘Yan Matan Fim Suka Samo Na Su GLK Din Ba, Amma Ni Tawa Baby Na Ne Ya Siya Min, Inji Samha M. Inuwa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Ni Dai Ban San Inda Sauran 'Yan Matan Fim Suka Samo Na Su GLK Din Ba, Amma Ni Tawa Baby Na Ne Ya Siya Min, Inji Samha M. Inuwa