Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma na Najeriya, Muhammad Idris Malagi ya buƙaci kowane ɓangare ya mayar da kubensa kan batun rufe gidan rediyon Badegi FM da ke birnin Minna a jihar Neja.
Ministan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Rabiu Ibrahim ya fitar, inda a ciki ya ce hukumar kafafen watsa labarai ta Najeriya wato NBC na da hanyoyin shiga tsakani idan aka samu irin wannan matsalar.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC na jihar a ranar 1 ga watan Agusta.
Gwamnan ya zargi gidan rediyon ya karya dokokin watsa labarai, da kuma tunzura mutane a kan gwamnatin jihar.
"Duk da cewa mun fahimci abin da gwamnatin ke zargi, ma'aikatar wa...
Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da sakacin da ta ce gwamnatin Najeriya na yi kan ɓacewar matashin ɗan gwagwarmaya, Abubakar Idris Dadiyata.
Amnesty International ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, inda ta ce tana mamakin yadda aka yi shekara shida ba tare da sanin halin da yake ciki ba.
Dadiyata ya ɓace ne a ranar 2 ga watan Agustan shekarar 2019, bayan wasu mutane ɗauke da makamai sun kutsa gidansa da ke unguwar Barnawa a Kaduna jim kaɗan bayan ya koma, suka suka tafi da shi.
"Tun lokacin ne iyalansa suke ta da jiran komawarsa, amma har yanzu da ya cika shekara shida babu bayani."
Shugaban ƙungiyar a Najeriya, Isa Sanusi ya ce shi kansa ya san Dadiyata a matsayin jajirtacce mai girmama na gaba.
"Mutane da dama, ciki har da...
Rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyar malaman jinya(Nurse) da Ungozoma ta Najeriya,(NANNM) sun janye yajin aikin gargadin da suke.
Sanarwar janye yajin aikin na kunshene a cikin takardar da shugaban kungiyar, Haruna Mamman da babban sakatarenta, T.A Shettima suka sakawa hannu.
Tun ranar Laraba ne dai kungiyar ta fara yajin aikin bayan karewar kwanaki 15 da ta baiwa gwamnati ta biya mata bukatunta.
Yajin aikin ya zo karshene bayan ganawar da kungiyar ta yi a yau Asabar.
A ranar Juma'ar data gabata, kungiyar ta yi zama na musamman da wakilan Gwamnati.
Matatar man Dangote ta nada David Bird mukamin CEO wanda zai jagoranci gudanarwar matatar.
S&P Global ne suka ruwaito hakan inda suka ce David Bird zai fara aiki a Watan Yuli.
Rahotanni sun ce David Bird Kwararren Injiniya ne wanda yayi aiki da kamfanin Shell na tsawon kusan shekaru 20.
Saidai har yanzu Dangote zai ci gaba da zama a matsayin mamallakin matatar man.
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Yahya Jingir kenan ya fashe da kuka yayin da yake Tafsir
Da yawa sun yiwa malam Addu'ar dacewa.
https://www.tiktok.com/@darul_burhan_majlis/video/7533716399286504760?_t=ZS-8yXmTkBArDt&_r=1
https://www.tiktok.com/@i_am_saeed01/video/7533722268485143864?_t=ZS-8yXmk6A0kb2&_r=1
Hadimin Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi, me suna Valentine Obienyem ya musanta cewa Ogan nasa ya shirya yiwa shugaba Tinubu juyin Mulki.
Ya zargi cewa, Wani me suna Arabambi ne ya kaiwa jami'an tsaro korafi akan Peter Obi da sauran wasu mutane irin su shugaban kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajaero, da sanata Victor Umeh da 'yar majalisar wakilai, Nenadi Usman.
Valentine yayi kiran a gudanar da bincike sannan a kama wanda yayi wannan yarfen dan a hukuntashi.
Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta ta rabawa 'yan Najeriya Miliyan 8.8 tallafi dan rage musu radadin talauci.
Gwamnatin tace zata raba wannan tallafi ne a mazabun dakw fadin kasarnan da suka kai 8,809.
A ranar Alhamis ne gwamnatin ta sanar da wannan shiri sannan tace za'a gudanar dashi ne a karkashin ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki.
Gwamnatin tarayyar tace, Kungiyar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta karfafa mata gwiwa wajan aiwatar da wannan aiki.
Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa'a ta wallafa Bidiyo ta tare da mijinta suna nishadi.
Ta wallafa Bidiyon ne a comment inda masoya ke yabawa yayin da wasu kuma ke kushewa.
https://www.tiktok.com/@backup_rashida_mai_saa/video/7533619313643670790?_t=ZS-8yXZfRLKsPR&_r=1
An samu wani yayi amfani da AI watau fasahar zamani na kwamfuta ko application yasa Maryam Labarina wadda tace ba zatawa mijinta wanke-wanke ba yin wanke wanken.
Tun bayan data furta wadannan kalaman a wani Podcast data bayyana a ciki lamarin ya dauki hankula sosai ake ta cece-kuce a akai.
Masu comment a kasan Bidiyon sun rika fadin an sa ta dai dole ta yi wanke-wanke.
https://www.tiktok.com/@yusufdahiru81/video/7533706665451900165?_t=ZS-8yXYjwgPbF2&_r=1