Saturday, December 13
Shadow

Duk Labarai

WANI DAN JAGALIYA YA CHÀKÀWÀ NI BABBAN SOJA WUKA HAR LAHIRA A GADAR KAWO TA JIHAR KADUNA

WANI DAN JAGALIYA YA CHÀKÀWÀ NI BABBAN SOJA WUKA HAR LAHIRA A GADAR KAWO TA JIHAR KADUNA

Duk Labarai
WANI DAN JAGALIYA YA CHAKAWA NI BABBAN SOJA WUKA HAR LAHIRA A GADAR KAWO TA JIHAR KADUNA. Rahotanni daga Jihar Kaduna sun tabbatar da cewar Wani babban jami’in soja, Laftanar Commodore M. Buba, ya rasa ransa bayan da wani ɓarawon waya ya soka masa wuƙa a ƙirji, Kuma ya rasa rayuwar sa har Lahira. Bala'in ya faru ne a gadar Kawo, lokacin da jami’in ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta fashe yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Jaji, inda yake karatu a Makarantar Horas da Sojoji ta Armed Forces Command and Staff College. Kakakin hukumar Yan'sanda ta kasa reshen Jihar Kaduna DSP Mansur Hassan ya tabbatar da aukuwar lamarin. Shedun gani da Ido sun ce Sojan ya hana barawon wayar ne kamar yadda ya bukata tun da farko, shi Kuma barawon ya zare wuka ya soka masa a kirji. ...
Kalli Bidiyo: Ba’amurkiya ‘Yar shekaru 68 ta auri matashi dan shekaru 25 a Najeriya

Kalli Bidiyo: Ba’amurkiya ‘Yar shekaru 68 ta auri matashi dan shekaru 25 a Najeriya

Duk Labarai
Wata mata ba'amurkiya me shekaru 68 ta zo Najeriya ta auri matashi dan shskaru 25. Matar tace a shafin facebook suka hadu inda tace ya fara liking wani comment da ta yi ne inda daga nan suka fara magana. https://www.youtube.com/watch?v=CNCGYAsOv9g?si=yCtzO2upWK8DXlTD Tace ta taso daga kasarta tazo Najeriya suka hadu da masoyinta kuma yace yana sonta.
Shugaban Kwamitin Da’a na majalisar Dattijai zai bar jam’iyyar sa ta Labour Party zuwa APC

Shugaban Kwamitin Da’a na majalisar Dattijai zai bar jam’iyyar sa ta Labour Party zuwa APC

Duk Labarai
Shugaban Kwamitin Da'a na majalisar Dattijai, Senator Neda Imasuen, wanda ya fito daga jihar Edo zai bar jam'iyyarsa ta Labour party zuwa jam'iyyar APC. Rahotanni ya shirya tsaf dan canja jam'iyyar tasa. Ya bayyana cewa, zai dauki wannan mataki ne saboda jam'iyyarsa ta Labour party ta rasa Alkibla. Yace kuma zai sanar da komawarsa jam'iyyar APC ranar 12 ga watan Yuni a birnin Benin City.
HAJJIN 2025: Yariman Saudiyya ya yi kira da kakkausar murya da a dakatar da kìsàn kìyàshì da ake wa Fàlàsɗìnàwà

HAJJIN 2025: Yariman Saudiyya ya yi kira da kakkausar murya da a dakatar da kìsàn kìyàshì da ake wa Fàlàsɗìnàwà

Duk Labarai
Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya kira ga al’ummar duniya da a dauki matakin dakatar da hare-haren da ake kai wa Gaza yana mai jaddada cewa akwai buƙatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin ta hanyar bin ka’idojin na duniya. Yariman Saudiyya ne ya yi wannan kira ga al’ummar duniya domin kawo karshen fadan da ake yi a Gaza. Kamfanin dillancin labarai na ƙasa ( NAN) ya rawaito sarki Salman na bayyana haka cikin saƙon da ya gabatar na taron shekara a lokacin a Muna a ranar Asabar. Ya jaddada cewa daukar mataki domin kare rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da kuma samar da yanayi na zaman lafiya da walwalar ga Falasɗinawa muhimmin abu ne. Ya ce, “wannan roƙi na nuna yadda kasar Saudiyya ta himmatu wajen kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa da...