Wednesday, April 1
Shadow

Duk Labarai

Bidiyo Da Duminsa: Yayin da ake rade-radin bashi da lafiya Shugaba Tinubu ya halarci taron majalisar zartaswa

Bidiyo Da Duminsa: Yayin da ake rade-radin bashi da lafiya Shugaba Tinubu ya halarci taron majalisar zartaswa

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya halarci taron majalisar zartaswa a fadarsa ranar Laraba. A taron, Shugaba Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar kula da gyaran dokoki. https://twitter.com/TheNationNews/status/1955627359089959341?t=FUtOhxqzj7DXoL6ye7uJBA&s=19 A baya dai an rika samun rahotanni masu cewa, Shugaba Tinubu bashi da lafiya har ana shirin fita dashi zuwa kasashen waje dan magani.
Ali Nuhu ya kaiwa gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya Ziyara inda yace za’a gina cibiyar yin fim a jihar sannan kuma za’a fara koyawa daliban jami’ar jihar gombe yin fim

Ali Nuhu ya kaiwa gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya Ziyara inda yace za’a gina cibiyar yin fim a jihar sannan kuma za’a fara koyawa daliban jami’ar jihar gombe yin fim

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, kuma shugaban hukumar fina-finai ta kasa, Ali Nuhu ya kaiwa Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya ziyara. Ali Nuhu yace ziyarar tasa sun tattauna muhimman baututuwa sannan ya samu tarba me kyau. Ali Nuhu yace daya daga cikin abubuwan da suka tattauna sune naganar gina cibiyar yin fim a jihar Gombe. Ali Nuhu yace cibiyar zata taimaka wajan karfafa fasaha musamman ta yin fim. Sannan yace akwai shiri na koyawa daliban jami'ar jihar Gombe yin film.
Yau wata guda kenan daidai da rashin shugaba Buhari, har yanzu ina jin zafin rashinsa, ji nake kamar yau ya rasu>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Yau wata guda kenan daidai da rashin shugaba Buhari, har yanzu ina jin zafin rashinsa, ji nake kamar yau ya rasu>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana alhinin tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari. Ya bayyana cewa, wata guda kenan da rasuwar shugaba Buhari inda yace Buhari ya kafa tarihi da rayuwa me nagarda wadda zata dawwama ana tunawa da ita. Ya bayyana cewa har yanzu zafin rashin Buhari bai gushe a zuciyarsa na dan ji yake kamar yaune Buharin ya rasu.
Gidana na Alfarma da ake ta cece-kuce akai na ginashi ne tun kamin in zama Minista>>Inji Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu

Gidana na Alfarma da ake ta cece-kuce akai na ginashi ne tun kamin in zama Minista>>Inji Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu

Duk Labarai
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu yayi martani kan rahotannin dake cewa ya gina gidansa ne a shekaru biyu bayan da ya zama Minista. Da yake magana ta bakin me magana da yawunsa, Mr. Femi Awogboro, Ministan yace maganar gaskiya ya kammala ginin gidanne a shekarar 2023, wata daya kamin a nadashi minista. Ministan ya kuma nuna hotuna a matsayin shaidar ikirarinsa inda yayi kiran cewa, tun kamin ya hau mukamin Minista ya gina gidan. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1955311072488964410?t=PdwSmz3RpdaUYga-kyaqdA&s=19 An dai rika tambayar ina ya samu kudin gina katafaren gida haka shekaru 2 kacal da zamansa minista?
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda ‘yan Najeriya suka shiga damuwa sosai bayan ganin kakakin majalisa, Godswill Akpabio yana tafiya da kyar yana dogara sanda

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda ‘yan Najeriya suka shiga damuwa sosai bayan ganin kakakin majalisa, Godswill Akpabio yana tafiya da kyar yana dogara sanda

Duk Labarai
An hango kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio yana tafiya da kyar yana dogara sanda bisa rakiyar mukarrabansa. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1955311072488964410?t=e_v88sFvmeE81bjCbMAz4g&s=19 Wasu dai sun rika cewa tsufa ne ke damunsa. A baya dai an rika yada rade-radin cewa bashi da lafiya.
Muna Magana da kasashen Saudiyya, Amurka, Ingila da sauransu dan samarwa matasa aiki yi a wadannan kasashe>>Gwamnatin Tarayya

Muna Magana da kasashen Saudiyya, Amurka, Ingila da sauransu dan samarwa matasa aiki yi a wadannan kasashe>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, suna aiki tare da kasashen Saudiyya, Amurka, Ingila da sauransu dan samarwa matasa aikin yi a wadannan kasashe. Ministan Gwadago, Muhammad Dingyadi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja. Yace suna horas da matasan wanda zasu je wadannan kasashe su yi aiki kuma abin ya amfane su da kasa baki daya. Ministan yace yanzu haka suna magana da daya daga cikin kasashen kuma sauran kasashen ma zasu ci gaba da neman wa matasan aikin a can.
Kalli Bidiyon yanda Ministan Wutar Lantarki ke nuna katafaren gidan daya gina yana Alfahari dashi

Kalli Bidiyon yanda Ministan Wutar Lantarki ke nuna katafaren gidan daya gina yana Alfahari dashi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Ministan Wutar Lantarkin, Adeboye Adelabu na ci gaba da shan caccaka saboda katafaren gidan da ya nuna wanda ya gina. Ya gina gidanne a Ibadan jihar Oyo inda aka ganshi a Bidiyon yana Alfahari da hakan. Da yawa dai sun rika tambayar ina ya samu kudin gina gida irin wannan a dan kankanin lokacin da yayi a matsayin minista? https://twitter.com/ChuksEricE/status/1955023808819233232?t=lPssTdurdmZH1IEhU8Sw6A&s=19