Saturday, April 4
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya karawa shugaban Kwastam wa’adi

Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya karawa shugaban Kwastam wa’adi

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya karawa shugaban Kwastam, Bashir Adeniyi yawan wa'adinsa. Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis. Sanarwar tace shugaban kwastam din, Mr. Bashir Adewale Adeniyi, MFR ya kamata ya ajiye aiki nan da 31 ga watan Augusta 2025. Amma an kara masa wa'adi zuwa shekara daya. Sanarwar tace an kara masa wa'adinne dan ya ci gaba da ayyukan gyara Najeriya sannan shugaba Tinubu ya yaba da aikinsa.
Gwamnati ta fara yiwa ‘yan ADC tayin Mukamai dan su yi watsi da jam’iyyar

Gwamnati ta fara yiwa ‘yan ADC tayin Mukamai dan su yi watsi da jam’iyyar

Duk Labarai
Tsohon shugaban jam'iyyar Hadakata ta ADC, Ralph Nwosu ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta masa tayin mukamin Minista har sau 3 dan ya bar jam'iyyar amma yaki. Ya bayyana hakane a ranar Talata a yayin da aka mikawa David Mark shugabancin jam'iyyar a hukumance. Yace kokarin na gwamnati yana son dakile kaifin duk wasu 'yan adawa ne dan mayar da Najeriya tsarin tafarkin jam'iyya daya. Yace an masa tayin kujerar Minista guda 3 ne dan ya dauki daya yayi kyauta da guda 2. Saidai yace ya zabi Dimokradiyyar Najeriya da ci gabanta. Ya kara da cewa, Najeriya ba zata zama kasa me jam'iyya daya ba bayan kokarin da aka yi na ganin an kawar da tsarin mulkin kama karya na soja. Yace tun bayan bayyana hadakatar 'yan Adawa a jam'iyyar ta ADC membobin jam'iyyar sun karu zuwa mutane Miliyan...
Idan Peter Obi ya dawo PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu wani dan takara daga Arewa da zai iya kayar dashi>>Inji Farfesa Jerry Gana

Idan Peter Obi ya dawo PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu wani dan takara daga Arewa da zai iya kayar dashi>>Inji Farfesa Jerry Gana

Duk Labarai
Farfesa Jerry Gana ya bayyana cewa idan Peter Obi ya koma PDP ya tsaya takarar shugaban kasa, babu dan takarar shugaban kasa daga Arewa da zai iya kayar dashi. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. Yace suna kan kokarin ganin sun jawo hankalin Peter Obi ya klma jam'iyyar su ta PDP. Yace kuma bayan Peter Obi din, akwai wani ma wanda yafi Peter Obi nagarta da karbuwa da suke kokarin kawowa PDP ya musu takara.
Wata Sabuwa: Kalli Bidiyon yanda Mai Wushirya ya yiwa wasu ‘yan Tiktok da ‘yan Kannywood dake Màdìgò tonon Silili, yace ko sallah basa yi

Wata Sabuwa: Kalli Bidiyon yanda Mai Wushirya ya yiwa wasu ‘yan Tiktok da ‘yan Kannywood dake Màdìgò tonon Silili, yace ko sallah basa yi

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Mai Wushirya ya yiwa wasu jaruman Kannywood da Tiktok mata wankin babban bargo inda ya zargi cewa suna lashe junansu. Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai inda aka ga yana cewa ko Sallah basa yi. Yace maza na kokarin neman na kansu su je su auresu amma sun lalata rayuwarsu har anko suke yi. Saidai har yayi ya gama fadansa bai kira suna ba. https://www.tiktok.com/@maiwushiryabackup/video/7532988026306186502?_t=ZS-8yTvjLes4nZ&_r=1 Hakan na zuwane yayin da kafar Tiktok din ta dauki dumi ake cece-kuce aka wani fada da ya barke a tsakanin wasu jarumai da ake zargi da Madigo.
Gwamnoni na farin ciki da cire tallafin man fetur kuma in ku baku jin dadi, su suna jin dadin cire tallafin>>Inji Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala

Gwamnoni na farin ciki da cire tallafin man fetur kuma in ku baku jin dadi, su suna jin dadin cire tallafin>>Inji Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala

Duk Labarai
Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala ya bayyana cewa, Gwamnonin Najeriya na jin dadin cire tallafin man fetur da aka yi. Yace a yanzu babu Gwamnan da baya iya biyan ma'aikatan jiharsa Albashi. Yace maimakon a baya wanda gwamnoni kusan sama da 20 ne basa iya biyan Albashi. Daniel Bwala ya bayyana hakane a yayin zantawar da aka yi dashi a gidan Talabijin na chan TV. Ya kuma ce gwamnonin a yanzu suna samun kudaden gudanar da ayyuka a jihohinsu ba kamar a baya ba.
Akwai yiyuwar in koma jam’iyyar APC, dan majalisa, Abdulmumin Jibrin bayan ganawa da Shugaba Tinubu

Akwai yiyuwar in koma jam’iyyar APC, dan majalisa, Abdulmumin Jibrin bayan ganawa da Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jiya. Bayan ganawar tasu a yayin da yake ganawa da manema labarai an tambayeshi ko haka na nuna cewa zai koma APC ne? Sai ya kayar da baki yace Yanzu ba lokacin wannan maganar bane, ya je ya gaishe da shugaba Tinubu ne sannan aun gana akan lamuran kasa, saidai yace abune mai yiyuwa ya iya komawa APC din. Ya kara da cewa hadin kai da zaman lafiyar Najeriya shine gaba da komai kuma ba abin mamaki bane ganinsa a fadar shugaban kasar.
Ku Daina Zagin Mahaifinsa in kuna yi bana jin dadi>>Inji Dan Gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai

Ku Daina Zagin Mahaifinsa in kuna yi bana jin dadi>>Inji Dan Gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan Gidan Tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai ya roki mutane da su daina zagin mahaifinsa inda yace idan ana yi baya jin dadi. Bashir Ya bayyana hakane a shafinsa na X. https://twitter.com/BashirElRufai/status/1950779372383723541?t=jVCVrXrS5CNdm0pMP-44Ng&s=19 Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na daga cikin 'yan siyasar da suka fi shan suka a Najeriya.
Ma’aikatan jinya sun fara yajin aiki a Najeriya

Ma’aikatan jinya sun fara yajin aiki a Najeriya

Duk Labarai
Ƙungiyar ma'aikatan jinya da unguzomomi ta Najeriya ta fara yajin aikin gargaɗi na mako guda a faɗin ƙasar. Ƙungiyar mai mambobi aƙalla 25,000 ta ca ta fara yajin aikin ne domin nuna rashin jin daɗinta kan rashin albashi mai kyau da ƙarancin ma'aikata da rashin biyansu alawus da kuma rashin kariya a wajen ayyukansu. Shugaban ƙungiyar, Morakinyo Rilwan ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa sun yanke shawarar fara yajin aikin ne bayan ƙarewar wa'adin kwanaki 15 da ƙungiyarsu ta bai wa gwamnati. Yajin aikin dai ya shafi ma'aikatan jinya da ungozomomin da ke aiki a asibitocin gwamnatin tarayya a cewar shugaban ƙungiyar. Mataƙin ma'aikatan jinyar na zuwa ne yayain da ake ci gaba da takun saƙa tsakanin ƙungiyar likitocin ƙasar da gwamnatin tarayya kan walwalar likitocin....
IMF tace tattalin arzikin Najeriya zai samu habaka

IMF tace tattalin arzikin Najeriya zai samu habaka

Duk Labarai
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta hasashensa kan bunƙasar tattalin arzikin Najeriya na shekarar 2025 da 2026. IMF ya bayyana sabon hasashen a watan Yulin da muke ciki wanda a ciki ya yi ƙiyasin samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Najeriya. Asusun ya yi hasashen samun jarin bunƙasar tattalin arzikin Najeriya da kashi 3.4 a 2025, ƙari a kan hasashen kashi 3.0 da ya yi a watan Afrilu. Haka kuma IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai samun ƙarin baunƙasa da kashi 3.2 a 2026, saɓanin hasashen kashi 2.7 da ya yi a watan na Afrilu.