Saturday, December 13
Shadow

Duk Labarai

An kama tsaffin shuwagabannin kamfanin man Fetur na kasa da aka sauke satin da ya gabata bisa zargin sun sace kudaden da aka ware dan gyaran matatun man Najeriya, An gano Naira Biliyan 80 a Asusun daya daga cikinsu

Rahotanni sun bayyana cewa, an kama tsaffin shuwagabannin matatun man fetur da aka sauke satin daya gabata saboda zargin sace kudaden da aka ware dan gyaran mamatun man fetur din. Matatun man fetur din sune Warri, Fatakwal da Kaduna. Jimullar kudaden da ake zarginsu da sacewa sun kai Dala $2,956,872,622.36. A matatar man fetur ta Fatakwal ana neman dala $1,559,239,084.36 a yayin da a matatar man fetur ta Kaduna ana neman dala $740,669,600 inda a matatar man Warri ana neman dala $656,963,938. Hakanan wata Majiya tace an samu Naira Biliyan 80 a asusun daya daga cikin manyan ma'aikatan. Ana dai zargin wadannan shuwagabannin da yaudarar 'yan Najeriya musamman game da gyaran matatar man Warri.
Nine ya kamata a zaba a matsayin sabon Fafaroma>>Inji Shugaban Amurka, Donald Trump Kiristoci sun zargeshi da batanci bayan da ya wallafa wannan hoton

Nine ya kamata a zaba a matsayin sabon Fafaroma>>Inji Shugaban Amurka, Donald Trump Kiristoci sun zargeshi da batanci bayan da ya wallafa wannan hoton

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, shine ya kamata a zaba a matsayin sabon Fafaroma bayan mutuwar Fafaroma Francis. An yi tsammanin shugaban da wasa yake, kwatsam da safiyar yau sai ga fadar White House ta wallafa hoton Trump sanye da kayan Fafaroma. Hakan ya harzuka kiristoci da yawa inda suka rika cewa, wannan batanci ne ga Addininsu.
Kalli Bidiyon fada a tsakiyar titin babban birnin tarayya Abuja inda mutum daya ya doke mutane 3 ya dauki hankula

Kalli Bidiyon fada a tsakiyar titin babban birnin tarayya Abuja inda mutum daya ya doke mutane 3 ya dauki hankula

Duk Labarai
Wani Bidiyon yanda fada ya kaure a tsakiyar titin babban birnin tarayya Abuja ya dauki hankula. Bidiyon ya nuna wani mutum da mutane 3 suka tarar masa amma duka ya gagaresu. https://twitter.com/abujastreets/status/1918291259908571165?t=t2fwv9g8VCD2370fkNWNMw&s=19 Saidai da dama sun bayyana mamakin faruwar irin hakan a tsakiyar Abuja.
Kalli Bidiyon Gwamnan jihar Osun yana rawa tare da mutanensa da suka dauki hankula

Kalli Bidiyon Gwamnan jihar Osun yana rawa tare da mutanensa da suka dauki hankula

Duk Labarai
Gwamman Jihar Osun, Ademola Adeleke kenan a wannan Bidiyon inda aka ganshi yana tika Rawa tare da wasu mutanensa a wajan motsa jiki. Lamarin ya dauki hankula duk da yake cewa ba yau ya fara rawa a bainar jama'a ba. https://twitter.com/AsakyGRN/status/1918055113672785996?t=CRdua9ANHmlPHeOHYHeKHA&s=19 Adeleke dai Kawune a wajan shahararren mawakin Najeriya, Davido.
Ka jawa Danka kunne yana wuce gona da iri>>Atiku ya gayawa Shugaba Tinubu bayan da aka zargi Seyi Tinubu da lakadawa shugaban Daliban Najeriya dukan kawo wuka

Ka jawa Danka kunne yana wuce gona da iri>>Atiku ya gayawa Shugaba Tinubu bayan da aka zargi Seyi Tinubu da lakadawa shugaban Daliban Najeriya dukan kawo wuka

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya jawo hankalin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya jawa iayalinsa musamman dansa, Seyi Kunne. Atiku yace Najeriya ba kayan Tinubu bane kasa ce ta al'umma dan haka bai kamata a bar dan shugaban kasar yana abinda yake ba na yawo yana nemawa mahaifinsa goyon baya ba. Atiku yace ya zama wajibi a binciki zargin da shugaban kungiyar daliban Najeriya ya yiwa Dan shugaban kasar dan gano gaskiya. Atiku yace kuma ko me ya faru da Shugaban daliban ba zasu amince ba zasu tsaya mai. Yace abin takaici ne ace irin wannan abin yana fitowa daga iyalin shugaban kasa. Atiku yace wannan abu ne da ba za'a amince dashi ba.
Ji yanda shugaba Tinubu ya kaiwa Sojojin dake Fagen yaki ziyarar ba zata ba tare da jami’an tsaronsa ba a jihar Katsina

Ji yanda shugaba Tinubu ya kaiwa Sojojin dake Fagen yaki ziyarar ba zata ba tare da jami’an tsaronsa ba a jihar Katsina

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kaiwa sojojin Najeriya na rundunar Operation FANSAR YAMMA dake yaki da 'yan Bindiga a jihar Katsina ziyarar ba zata dan ya ga yanda ake gudanar da aiki. Shugaban ya je ne ba tare da jami'an tsaronsa ba kamar yanda aka saba. Ya karfafa sojojin musamman yanda suka sadaukar da rayuwarsu dan samarwa mutanen Najeriya tsaro. Yace zasu yi kokarin biyan sojojin dukkanin hakkokinsu da kuma inganta rayuwarsu data iyalinsu.