Iyalan Mafarautan Da Aka Kàshè A Edo Sun Yi Zanga-zangar Neman Diyya
Iyalan Mafarautan Da Aka Kashe A Edo Sun Yi Zanga-zangar Neman Diyya.
Iyalan wasu mafarauta da suka rasa rayukansu a harin da ya faru a jihar Edo sun gudanar da zanga-zanga domin neman a biya su diyyar ‘yan uwansu da kuma gurfanar da wadanda suka aikata wannan mummunan laifi.
Zanga-zangar, wadda ta gudana kwanaki 40 bayan aukuwar lamarin, ta samu halartar daruruwan ‘yan uwa da abokan arziki na wadanda abin ya shafa, wadanda suka fito dauke da takardu da hotunan wadanda suka mutu suna rokon gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa.
Wani daga cikin shugabannin iyalan, ya bayyana cewa:"Har yanzu ba a kama ko daya daga cikin wadanda suka aikata wannan kisa ba. Mun gaji da jiran shiru. Muna so a tabbatar mana da adalci kuma a tallafa mana da diyya domin wadanda suka bar...








