Friday, December 19
Shadow

Duk Labarai

Idan dai za’a yi zaben gaskiya, Peter Obi baya bukatar Atiku ko El-Rufai kamin ya kayar da Tinubu>>NLC

Idan dai za’a yi zaben gaskiya, Peter Obi baya bukatar Atiku ko El-Rufai kamin ya kayar da Tinubu>>NLC

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta bayyana cewa, idan dai za'a yi zaben gaskiya, Peter Obi baya bukatar Hada kai da Atiku Abubakar ko El-Rufai kamin yayi nasara kada Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027. Mataimakin shugaban NLC ne ya bayyana hakan inda yace a zaben 2023, Peter Obi ya kama hanyar nasara kamin a samu tangardar da ta canja lamarin. Yace indai hukumar zabe me zaman kanta, INEC ba zata yi Magudi ba, to Peter Obi yana da karfin mabiyan da zai lashe zaben 2027.
EFCC ta tsare mutane biyu bisa samun su da kuɗaɗen kasashen waje a Kano

EFCC ta tsare mutane biyu bisa samun su da kuɗaɗen kasashen waje a Kano

Duk Labarai
EFCC ta tsare mutane biyu bisa samun su da kuɗaɗen kasashen waje a Kano. Hukumar EFFC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta fara bincike kan wasu dubun dubatar kuɗaɗen ƙasar waje da aka kama a filin jirgin sama na Kano. BBC ta rawaito cewa, EFCC ta ce an ga dala 86,500,305 da kuma riyal 305,150 ne cikin wata jaka lokacin da aka ga wani ma'aikacin filin jirgin mai suna Sale Bala ya yi yunƙurin ɗaukar ta ranar Lahadi. "Bayan bincike, jami'an kwastam sun gano kuɗaɗen ne da aka ɓoye cikin zannunwan gado," in ji EFCC cikin wata sanarwa. "An kama Sale Bala da wani Abdullahi Tahir da ake zargin shi ne aka tsara zai karɓi jakar bayan kammala tantance ta." Ta ƙara da cewa kuɗin da kuma waɗanda ake zargi na tsare a hannunta, kuma za ta kai su kotu da zarar an kammal...
Atiku Abubakar na shirin barin PDP

Atiku Abubakar na shirin barin PDP

Duk Labarai
Atiku Abubakar 2011 President campaign Photo by www.mortenfauerby.dk ©mortenfauerby 2010 - all rights reserved Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa, Abokin takararsa Atiku Abubakar ma na shirin barin PDP. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. Da aka tambayeshi ko ya sanar da Atiku maganar ficewarsa daga PDP Yace ya sanar dashi zasu yi zama na musamman dan nemawa kansu mafakar siyasa. Yace Atiku ma ya alamta cewa yana shirin barin jam'iyyar PDP.
Da yawan ‘yan majalisa basa iya biyan Kudin makarantar ‘ya’yansu>>Inji Sanata Na’Allah

Da yawan ‘yan majalisa basa iya biyan Kudin makarantar ‘ya’yansu>>Inji Sanata Na’Allah

Duk Labarai
Tsohon sanata daga jihar Kebbi Sanata Bala Ibn Na'Allah ya bayyana cewa da yawan 'yan majalisa bayan sun bar majalisar basa iya biyan kudin makarantar 'ya'yansu. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Trust TV. Yace yawanci 'yan majalisa idan suka yi ritaya bayan shekara daya zaka ga basa iya biyan kudin makarantar 'ya'yansu. Yace wannan yana faruwane musamman ga wadanda dama can basu da wata sana'a sai siyasar. Yace yawanci mutane suna tsammanin wasu manyan kudi ne ake samu a majalisar Amma a gaskiyar zahiri ba haka bane.
Kalli Bidiyo: Cikin sheshshekar kuka wannan matar tana rokon Dan Allah wani ya fito ya aureta, tace Wallahi ta tuba ba zata kara yin rawar badala a intanet ba, tace kuma zata baiwa duk wanda ya yadda ya aureta naira Miliyan 20

Kalli Bidiyo: Cikin sheshshekar kuka wannan matar tana rokon Dan Allah wani ya fito ya aureta, tace Wallahi ta tuba ba zata kara yin rawar badala a intanet ba, tace kuma zata baiwa duk wanda ya yadda ya aureta naira Miliyan 20

Duk Labarai
Wannan matar dake da shekaru sama da 40 ta fito tana kuka tana cewa ta tuba da rawar badala da take yi a kafafen sada zumunta. Matar tace yanzu mijin aure take nema. Tasha Alwashin bayar da Naira Miliyan 20 ga duk wanda zai aureta: Kalli Bidiyon a kasa: https://twitter.com/Teeniiola/status/1916953355559047646?t=yHCWKxtVQd6mqw5KWpM6uQ&s=19 Ko kana ciki?