Wednesday, November 19
Shadow

Da yawan ‘yan majalisa basa iya biyan Kudin makarantar ‘ya’yansu>>Inji Sanata Na’Allah

Tsohon sanata daga jihar Kebbi Sanata Bala Ibn Na’Allah ya bayyana cewa da yawan ‘yan majalisa bayan sun bar majalisar basa iya biyan kudin makarantar ‘ya’yansu.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Trust TV.

Yace yawanci ‘yan majalisa idan suka yi ritaya bayan shekara daya zaka ga basa iya biyan kudin makarantar ‘ya’yansu.

Yace wannan yana faruwane musamman ga wadanda dama can basu da wata sana’a sai siyasar.

Yace yawanci mutane suna tsammanin wasu manyan kudi ne ake samu a majalisar Amma a gaskiyar zahiri ba haka bane.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Ba yaran nan kadai, har iyayensu ya kamata Shugaba Tinubu ya karramasu>>Inji Sheikh Gadon Kaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *