Yajin aikin ma’aikatan NIMET ya hana wasu jirage tashi a Najeriya
Harkokin sufurin jiragen sama na fuskantar cikas a filayen tashi da saukar jiragen sama na cikin gida yayin da ma'aikatan hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ke gudanar da yajin aikin kan rashin ingancin yanayin aiki.
Yajin aikin da ya yi kwana biyu yana gudana ya haifar da maƙalewar fasinjoji a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, da filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas da sauran filayen jiragen sama da ke faɗin ƙasar.
Kamfanin sufurin jiragen sama mafi girma a Najeriya, Air Peace ya sanar da dakatar da ayyukansa sakamakon yajin aikin.
Kamfanin ya sanar da cewa ya yanke shawarar dakatar da sufurin jiragensa ne saboda kiyaye rayukan fasinjojinsa.
Kafar yaɗa labarai ta Channels ta rawaito cewa a filin jirgin saman Legas, kamfanin XEJET da Aero Contractors, d...








