Friday, May 1
Shadow

Duk Labarai

Masu ikirarin Jìhàdì sun kàshè sojojin Najeriya hudu a sabbin hare-haren da suka kai Borno

Masu ikirarin Jìhàdì sun kàshè sojojin Najeriya hudu a sabbin hare-haren da suka kai Borno

Duk Labarai
Mayaƙan IS sun ƙara kai wa sojojin Najeriya hari, karo na biyu a cikin kwanaki biyu. Rundunar sojin Najeriya ta ce maharan sun kashe dakarunta huɗu a wani sansanin su da ke kusa da garin Rann da ke kan iyakar ƙasar da Kamaru a ihar Borno. A ranar Litinin ma IS ta kai hari a wani sansanin soji da ke yammacin Borno, a garin Marte, inda aka bayar da rahoton kisan sojojin Najeriya da dama. Masu sharhi sun ce a baya bayan nan mayaƙan masu iƙirarin jihadi sun canza salon kai hare-hare, ciki harda amfani da jirgin sama marar matuƙi.
Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya

Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya

Duk Labarai
Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka mai neman tabbatar da tsarin karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya. Wannan na daga cikin aikin da majalisar ke yi na gyaran wasu sassa shida na kundin mulkin ƙasar, waɗanda a baya suka gaza tsallake karatu na biyu a zauren majalisar. Zaman majalisar na ranar Talata wanda shugabanta Abbas Tajudeen ya jagoranta ya yi muhawara a kan ƙudirin sannan ya cimma matsayar yin watsi dashi kamar yadda ya yi wa sauran ƙudirorin da aka gabatar da su tare. Sai dai ana sa ran batun zai ƙara tasowa a zaman majalisar wakilan na yau Laraba domin sake tafka muhawa da ɗaukar matsaya a kai. Wasu daga cikin ƴan majalisar da suka yi muhawara a kan ƙudirin sun ce a yanzu haka jam'iyyun siyasar Najeriya suna da irin nasu tanadi na tantance karɓa-karɓan shu...
Mun Gano Tabbas ‘yan Tà’àddà  na Amfani da Jirage marasa matuka irin na kasashen Israela da Ukraine>>Sojojin Najeriya suka koka

Mun Gano Tabbas ‘yan Tà’àddà na Amfani da Jirage marasa matuka irin na kasashen Israela da Ukraine>>Sojojin Najeriya suka koka

Duk Labarai
Rundunar soji ta Operation Hadin Kai ta koka da yanda tace masu ikirarin Jihadi na Kungiyar B0k0 Hàràm na amfani da jirage marasa matuka dan kai musu hari. Rundunar tace irin wannan hare-haren na da wahalar ganowa da dakilewa musamman ta hanyar amfani da hanyoyin da aka saba wadanda ba na zamani ba. Shugaban Rundunar, Major General Abdulsalam Abubakar ne ya bayyana hakan a wajan wani taro a Maiduguri. Yace wasu daga cikin jiragen marasa matuka da kungiyar ke amfani dasu na kama da irin wadanda ake amfani dasu a kasashen Israela da Ukraine. Dan haka ya jawo hankalin sauran 'yan kungiyar dasu tuba su mika kansu ga jami'an tsaro kamar yanda 'yan uwansu ke yi kuma ana karbar su tare da cin zarafi ba. Saidai yayi gargadin wadanda suka ki amincewa su mika kansu, zasu fuskanci ki...
Ba ‘yan Bindiga bane mune: Hukumar ‘yansandan Najeriya ta yi karin haske kan Jirgin samansu da aka gani a daji

Ba ‘yan Bindiga bane mune: Hukumar ‘yansandan Najeriya ta yi karin haske kan Jirgin samansu da aka gani a daji

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya ta yi karin haske kan Bidiyon da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga jirgin samansu yana sauka da tashi a tsakanin wasu masu rike da makamai. An yi zargin cewa jirgin ya je kaiwa 'yan Bindiga kayan abinci da sauran kayan aiki ne. Saidai a sanarwar da ta fitar ta shafinta na sada zumunta, Hukumar 'yansandan tace ba 'yan Bindiga bane aka gani a cikin Bidiyon ba. 'Yansanda ne dake aikin samar da tsaro a dajin Obajana na jihar Kogi. Hukumar tace a daina dogaro da bayanan da basu fito daga bakin hukumomin tsaro ba dan gujema labarin karya.
Ana rade-radin ba’a ga Fatima Me Zogale ba a wajan Bikin Rarara da A’ishatulhumaira ba

Ana rade-radin ba’a ga Fatima Me Zogale ba a wajan Bikin Rarara da A’ishatulhumaira ba

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Ko Kun Hango Fuskar Fatima Mai Zogale Tun Daga Lokacin Da Aka Soma Hada-Hadar Bikin Rarara Da Aisha Humaira Har Aka Kammala?
Kalli Bidiyo: In Kunsan ba zaku iya yàkì ba gara ku fada>>Sojan Najeriya ya gayawa Abokan aikinsa sojoji da suka tsere daga sansaninsu na Marte bayan da ‘yan tà’àddà suka afka musu

Kalli Bidiyo: In Kunsan ba zaku iya yàkì ba gara ku fada>>Sojan Najeriya ya gayawa Abokan aikinsa sojoji da suka tsere daga sansaninsu na Marte bayan da ‘yan tà’àddà suka afka musu

Duk Labarai
Bayan mummunan harin da kungiyar masu ikirarin jihadi ta ÌŚWÀP suka kaiwa sansanin sojojin Najeriya a Marte, an ga Bidiyon wani soja da yake kokawa kan irin barnar da aka musu. Sojan ya nuna cewa an kone musu motocin yaki sannan an kashe sojoji 4. Ya kara da cewa yana kira ga abokan aikinsa idan sun san ba zasu iya yaki ba gara su fadi. Kalli Bidiyon a kasa: https://twitter.com/General_Somto/status/1922331821385080970?t=RnPeB4ry_AyxjmYSnpyDHw&s=19 Wasu rahotanni sun ce kungiyar ta kuma tafi da wasu sojoji da ta yi garkuwa dasu.
Shahararriyar ‘yar Najeriya me yin fina-finan Bàtsà ‘yar Najeriya, Mààmì Igbagbo tace ta tuba ta koma Kirista kuma tana fatan Allah ya yafe mata

Shahararriyar ‘yar Najeriya me yin fina-finan Bàtsà ‘yar Najeriya, Mààmì Igbagbo tace ta tuba ta koma Kirista kuma tana fatan Allah ya yafe mata

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shahararriyar me fina-finan batsa ta Najeriya, Maami Igbagbo tace ta tuba ta koma Kirista kuma tana fatan Allah ya yafe mata. Ta bayyana hakanne a wani Bidiyo da aka yi hira da ita inda tace ta yi nadamar irin rayuwar da ta yi a baya. Saidai tambayar da mutane ke yi shine ko za'a samu wanda zai iya aurenta kasancewar ga Bidiyon ta ya karade ko ina ana ta ganin ta na aikata Alfasha?
Bidiyon da aka yi zargin An ga jirgin sama na kaiwa ‘yan Bìndìgà a daji makamai ya dauki hankula

Bidiyon da aka yi zargin An ga jirgin sama na kaiwa ‘yan Bìndìgà a daji makamai ya dauki hankula

Duk Labarai
Wani Bidiyo ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga wani jirgin sama me saukar Angulu yana tashi a Daji da mutane da yawa. An dai yi zargin cewa, 'yan Bindiga ne aka kaiwa makamai a cikin jirgin. https://twitter.com/ubasinachimbia/status/1921978044962443621?t=SfCf-io98qlxaLCgJ9J9cA&s=19 Saidai babu wata kafa me inganci data tabbatar da hakan.
Ina zuwa Masallaci, da Coci da gurin masu bautar Gumaka saboda nasan duk dai Allah daya ake bautawa>>Inji Mawakin Najeriya, Portable

Ina zuwa Masallaci, da Coci da gurin masu bautar Gumaka saboda nasan duk dai Allah daya ake bautawa>>Inji Mawakin Najeriya, Portable

Duk Labarai
Mawakin Najeriya me yawan jawo cece-kuce, Portable ya bayyana cewa yana zuwa kusan duka guraren ibada da ake dasu a Najeriya, watau Masallaci, Coci, da wajan masu Bautar Gumaka. Yace dalilinsa na yin hakan shine yasan duk Allah daya ake bautawa. Yace yana rokon Allah kuma Allah na amsa mai du'a'insa.