Sai Tinubu ya yi sa’a ma zai zo na uku a zaɓen 2027— In ji El-Rufai
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ba ya damu da yawan sauya sheƙa da ake yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a shirin Arise TV a daren Litinin, El-Rufai ya ce shugaban ƙasa mai ci yana ɗaukar matsayin cewa tuni an gama da dawowar sa karo na biyu, ganin yadda wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa ke sauya sheƙa zuwa APC.
Sai dai ya bayyana cewa: "Tinubu ba zai ci zaɓe ba. A gaskiya, zai yi sa’a idan ma ya zo na uku."
Tsohon gwamnan ya zargi gwamnatin Tinubu da halin ko in kula dangane da matsanancin halin tsaro da ƙasar ke ciki, yana mai bayyana cewa an cire naira biliyan 100 daga Asusun Tarayya cikin watanni 15 da suka gabata ba tare da amincewar jihohi ko majalisar dokoki ba.
Ya ce: "Tun cikin watanni 15 da suka wuce, ana...


