Saturday, May 2
Shadow

Duk Labarai

Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa dan magance matsalar barin Jam’iyyar da ake ta yi

Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa dan magance matsalar barin Jam’iyyar da ake ta yi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Jam'iyyar PDP sun kira wani taro na musamman da zai tattauna rikicin dake cikin jam'iyyar da yasa mutane ke ta fita daga cikinta. Gwamnonin sun kira tsaffin Gwamnonin Jam'iyyar da tsaffin shuwagabannin majalisun tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyyar dan tattaunawa kan yanda za'a shawo kan wannan matsala. Jam'iyyar PDP na fama da matsalar ficewar da yawa daga cikin membobinta zuwa jam'iyyar APC me mulki. Na baya-bayannan sune komawar Gwamnan Jihar Delta,b Sheriff Oborevwori da Tsohon Gwamnan jihar kuma tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Ifeanyi Okowa zuwa jam'iyyar APC. Hakanan duka sanatocin jihar Kebbi su 3 suma sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC da sauransu.
Tsadar Rayuwa da Man fetur tasa masu motocin Alfarma matsu tsada sun koma yin haya dasu a Najeriya, ciki hadda sojoji, da ma’aikatan banki da sauransu

Tsadar Rayuwa da Man fetur tasa masu motocin Alfarma matsu tsada sun koma yin haya dasu a Najeriya, ciki hadda sojoji, da ma’aikatan banki da sauransu

Duk Labarai
Tsadar rayuwa tasa masu motocin Alfarma masu tsada ciki hadda sojoji da ma'aikatan banki da sauransu sun koma yin haya da motocin nasu dan samun sauki. Tun da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta cire tallafin man fetur, tsadar rayuwa ta kara kazancewa a Najeriya. An zanta da wasu daga cikin ma'aikatan Gwamnati da suka koma daukar fasinja dan samun saukin rayuwa. Jaridar Punchng tace wakiliyarta a Legas ta zanta da wasu daga cikin masu irin wannan sana'ar. Akwai soja akwai ma'aikatan banki akwai ma 'yan kasuwa da Sauransu wadanda jaridar ta zanta dasu inda suka bayyana cewa sukan dauki fasinjoji ne dan samun saukin musaman kudin Ma fetur, wasu kuma sun ce suna hakanne dan samun karin kudin da zasu kula da iyalinsu saboda albashi baya isarsu. A baya da mun ga yanda...
Makaho ne kawai zai ce Tinubu baya kokari>>Inji Wike

Makaho ne kawai zai ce Tinubu baya kokari>>Inji Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike yace makaho ne kawai zai ce shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu baya kokari. Wike ya bayyana hakane yayin da yake ran gadin wasu ayyukan da ake gudanarwa a Abuja. Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kawo ayyuka masu kyau da inganci Abuja inda yace kowa ya shaida hakan. Abuja ta canja. Ya karkare da cewa, Makaho ne kadai zai ce Tinubu bai yi kokari ba.
Bidiyo:Kalli Yanda wadannan ‘yan matan ke kuka suna bayar da labarin yanda faston su ya dirka musu cikkunan shege

Bidiyo:Kalli Yanda wadannan ‘yan matan ke kuka suna bayar da labarin yanda faston su ya dirka musu cikkunan shege

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wasu 'yan mata sun bayyana inda suke bayar da labarin yanda fastonsu ya dirka musu cikkunan shege. Daya daga cikisu hadda kuka inda take cewa yayi amfani da ita ya yadda ta. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1921285781336768975?t=xDvA9rkk_pR8tdhOvXOFCw&s=19 Lamarin dai ya baiwa mutane mamaki.
El-Rufai da Peter Obi Sun Tattauna a Gefen Taron Cambridge Africa Together a Birtaniya

El-Rufai da Peter Obi Sun Tattauna a Gefen Taron Cambridge Africa Together a Birtaniya

Duk Labarai
YANZU-YANZU: El-Rufai da Peter Obi Sun Tattauna a Gefen Taron Cambridge Africa Together a Birtaniya. An hango tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, na tattaunawa da ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, a gefen taron shekara-shekara karo na 11 na Cambridge Africa Together Conference (ATC), wanda ke gudana a Jami’ar Cambridge, ƙasar Birtaniya. Taron, wanda ke ɗaya daga cikin manyan taruka da ke haɗa shugabanni, masana da matasa daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka da duniya, ya kasance dandali na musayar ra’ayoyi, tattaunawa kan ci gaban Afirka, shugabanci da sabbin dabaru na magance matsalolin da ke fuskantar nahiyar. El-Rufai da Peter Obi, wadanda dukkansu sanannu ne a harkar siyasar Najeriya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen ...