Duk rintsi muna tare da Kashim Shettima>>Rahama Sadau bayan dambarwar data faru inda Ganduje ya kira sunan shugaba Tinubu ba tare da kiran sunan Kashim Shettima ba
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta bayyana cewa, duk rintsi suna tare da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Ta bayyana hakanne a shafinta na sada zumunta.
Hakan na zuwane bayan da aka zargi shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kiran sunan Tinubu ba tare da hadawa da Kashim Shettima ba a wajan yakin neman zabe.
Lamarin ya jawo hatsaniya wanda da kyar aka fitar da Gandujen daga wajan taron.








