Friday, July 24
Shadow

Yanda Rikici ya tashi a majalisar wakilai yayin karatun kudirin dokar kafa ‘yansandan jihohi

A jiyane dai majalisar wakilai ta amince da kudirin dokar kafa ‘yansandan jihohi.

Saidai bangaren marasa rinjaye na majalisar sun bayyana rashin amincewa da yanda aka gabatar da kudirin dokar.

Me magana da yawun marasa rinjaye na majalisar, Afam Ogene ya bayyana cewa, Abu na farko da ya damesu shine maganar sunayen wadanda suka halarci zaman da aka kira.

Yace da yawa cikin sunayen da aka kira basu sansu ba, yace bisa al’ada ana kiran sunayen wadanda ke cikin majalisar ne ta hanyar daukar rijistar da suke sakawa hannu idan sun je wajan aiki amma a jiyan ba haka aka yi ba.

Karanta Wannan  Duk Wanda Ya Yi Silar Haduwata Da Adam A. Zango, Na Yi Alkawarin Zan Ba Shi Tukwicin Naira Dubu Dari Biyar, Inji Matashi Sharhabilu Musa Malumfashi

Ya kuma zargi kakakin majalisar da karya doka ta hana ‘yan majalisar dubawa kudirin dokar dan samun damar kawo gyara ga kudirin dokar kamin a amince dashi.

Shima shugaban marasa Rinjaye na majalisar, Frederick Agbedi ya bayyana cewa, Maganar amincewa da kudirin dokar kafa ‘yansandan jihohi an musu rufa-rufa.

Yace an hanasu su karanta kudirin dokar da kuma bayar da gudummawa akan sa, yace shiyasa suka fita yayin da ake dubashi.

Ya kara da cewa an ce sun amince da kudirin dokar, to idan sun fita daga majalisar ta ya hakan zai yiyu?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *