Saturday, July 18
Shadow

Duk Labarai

Maza sama da 50 na taimakawa na koyama Jima’i wanda basu taba sanin mace ba>>Inji Wannan matar

Maza sama da 50 na taimakawa na koyama Jima’i wanda basu taba sanin mace ba>>Inji Wannan matar

Duk Labarai
Wata mata me suna Gigi Patsy 'yar Komanin shekaru 29 ta bayyana cewa, maza sama da 50 ne ya lalata ta hanyar koya musu yanda ake Jima'i. Ta bayyana cewa ta hadu da maza sama sa 2000. Saidai tace abin mamaki a cikinsu akwai sama da 50 wanda basu taba sanin mace ba. Tace kuma ba wai matasa bane kadai hadda wadanda suka haura shekari 30 zuwa 50. Tace wasu zasu je su ce mata ko kiss basu taba yiwa mace ba kuma haka zata hakura ta fara koyar dasu. Tace wasu addini, da al'ada da kunya na taimakawa wajan rashin iya jima'insu. Tace amma duk tana koyar dasu.
Gwamnatin Kano na da kudin da ta fi Karfin Haka: Shehu Sani yace Naira Miliyan daya da Gwamna Abba yace a baiwa kowane iyalan ‘yan kwallon Kano da suka ràsù a hadarin mota ta yi kadan

Gwamnatin Kano na da kudin da ta fi Karfin Haka: Shehu Sani yace Naira Miliyan daya da Gwamna Abba yace a baiwa kowane iyalan ‘yan kwallon Kano da suka ràsù a hadarin mota ta yi kadan

Duk Labarai
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, Naira Miliyan 1 da Gwamnatin Kano tace a baiwa kowane daga cikin iyala 'yan Kwallon jihar da suka yi hadari ta yi kadan. Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace Gwamnatin jihar Kano na da kudin da ya kamata ace abinda zata bayar yafi haka. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da yake aikin hajji, ya ce a baiwa kowane daga cikin iyalan 'yan kwallon Naira Miliyan 1 sannan a basu kayan abinci kamin ya dawo.
Bidiyon wani mahajjacin Najeriya na kiran Shehu a Kasar Saudiyya ya jawo cece-kuce

Bidiyon wani mahajjacin Najeriya na kiran Shehu a Kasar Saudiyya ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Bidiyon wani Mahajjaci a kasar Saudiyya dake cikin mahajjatan Bana yana kiran Shehu ya dauki hankula. https://twitter.com/_mai_daraja/status/1928928524502487253?t=mGvwrKfhfp7oqNc1-89GmA&s=19 Lamarin yasa mutane na bayyana cewa yayi asarar Naira Miliyan 8 da wani abu da ya biya ya je aikin Hajjin. Menene ra'ayinku?
Gwamnan jihar Akwa-Ibom ya magantu bayan da diyarsa ta zargeshi da yunkurin kàshè ta da yin tsafi da ita da diyarta

Gwamnan jihar Akwa-Ibom ya magantu bayan da diyarsa ta zargeshi da yunkurin kàshè ta da yin tsafi da ita da diyarta

Duk Labarai
Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Umo Eno ya bayyana cewa, babu wata matsala a cikin iyalinsa, bayan da diyarsa ta zargi cewa yana yunkurin kashe ta da diyarta dan yin tsafi dasu. Diyar Gwamnan me suna Jane, ta zargi cewa, haka mahaifiyarta da 'yan uwanta biyu suka mutu inda ake zargin baban nasu da kashesu ta hanyar tsafi. Saidai a martaninsa, Gwamnan yace ana kokarin kawar masa da hankali ne a aikin da yake yi a matsayinsa na Gwamna. Yace wannan tsohon bidiyone kuma a yanzu da yake kokarin bayyana irin ayyukan da gwamnatin sa ta yi a cikin shekaru 2 da yayo yana Gwamna, shine aka dauko tsohon bidiyon ana yadawa.
A yau Lahadi, Masana Kimiyya sun ce wani Mulmule daga Rana zai fado Duniyarmu inda zai iya lalata wutar Lantarki, da Intanet

A yau Lahadi, Masana Kimiyya sun ce wani Mulmule daga Rana zai fado Duniyarmu inda zai iya lalata wutar Lantarki, da Intanet

Duk Labarai
Masana sararin samaniya na kasar Amurka, NOAA sun bayyana cewa, akwai yiyuwar wani mulmule daga rana zai fado Duniyarmu a yau Lahadi. Sun bayyana cewa, mulmulen na da sauri sosai inda yake gudun kisan Kilometres 1000 a duk sakan ko dakika. Sun ce zuwansa Duniyar mu ka iya shafar wutar lantarki da yadda Intanet ke aiki. Saidai basu bayyana a wane yanki ne zai fado ba.
Mu Dai Mun bi: Tinubu zamu zaba a shekarar 2027, Inji Gwamnan Legas inda yace farashin kayan abinci yayi kasa

Mu Dai Mun bi: Tinubu zamu zaba a shekarar 2027, Inji Gwamnan Legas inda yace farashin kayan abinci yayi kasa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Legas, Sonwo Olu ya bayyana goyon bayansa ga zarcewar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027. Ya bayyana hakane a yayin da yake jawabi ga ma'aikatan jihar Legas din inda yace yana aiki ne tukuru wajan inganta rayuwar su. Yace ana ganin alfanun tsare-tsaren gwamnatin Tinubu inda yace misali an samu ci gaba ta fannin noma, farashin kayan abinci ya sauka.
APC ta zargi cewa ‘yan Adawa ne ke daukar nauyin harè-hàrèn da ‘yan Bìndìgà ke kaiwa dan kawai ace Tinubu bai iya mulki ba baya kokari

APC ta zargi cewa ‘yan Adawa ne ke daukar nauyin harè-hàrèn da ‘yan Bìndìgà ke kaiwa dan kawai ace Tinubu bai iya mulki ba baya kokari

Duk Labarai
Jam'iyyar APC, ta yi zargin cewa, Wasu 'yan Adawa ne ke daukar nauyin 'yan Bindigar dake kai munanan hare-hare a fadin Najeriya dan a karya lagon Gwanatin shugaba Tinubu. Hakan ya fito ne daga bakin daya daga cikin masu ruwa da tsaki na APC a jihar Osun, retired Brig.- Gen. Bashir Adewinbi. Saidai yace shugaba Tinubu ya tashi tsaye haikan yana kokarin magance wannan matsala. Ya bayyana hakane yayin wata ziyara da mata 'yan APC suka kai masa. Yace gwamnatin Tinubu na son amfani da makamai na zamani dan magance matsalar tsaron da ake fama da ita.
An gargadi su El-Rufai,Atiku, da Peter Obi su daina zuga ‘yan Najeriya game da Gwamnatin Tinubu kar su kawo tarnaki

An gargadi su El-Rufai,Atiku, da Peter Obi su daina zuga ‘yan Najeriya game da Gwamnatin Tinubu kar su kawo tarnaki

Duk Labarai
An gargadi su Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, da Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, da Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi su daina zuga 'yan Najeriya kan mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Wani dattijon jihar Legas, Chief Adesunbo Onitiri ne ya bayyana hakan a wata ganawa dashi. Yace irin maganganun da wadannan 'yan siyasar ke yi na iya kawo tarnaki wa tsarin siyasar kasarnan. Yace su rika saka kishin kasa da al'ummarsu a cikin kalamansu. Yace musamman Atiku dake neman ya binciko wasu laifukan shugaban kasar daga kasar Amurka dan hanashi takara a zaben shekarar 2027, yace hakan ba daida bane kuma ba zasu amince da hakan ba.
Ƙasar Saudiyya Za Ta Fassara Hudubar Aikin Hajjin Bana Da Yaren Hausa A Ranar 9 Ga Watan Zul-Hajj

Ƙasar Saudiyya Za Ta Fassara Hudubar Aikin Hajjin Bana Da Yaren Hausa A Ranar 9 Ga Watan Zul-Hajj

Duk Labarai
Za a fassara Hudubar Hajj ta shekarar 1446 zuwa harsuna 34 a ranar Alhamis, 9 ga Dhul Hijjah 1446, kamar yadda shafin Haramain Sharifain ya rawaito. Harsunan su ne kamar haka: Larabci Urdu Turanci Faransanci Indonesiyanci Farisanci (Farsi) Hausa Sinanci (Mandarin) Rashanci Bengalanci Turkiyanci Malayyanci (Bahasa Melayu) Sifaniyanci Fotugis Italiyanci Jamusanci Filipino (Tagalog) Amharic (Habasha) Bosniyanci Hindi Dutch Thai Malayalam Suwahili Pashto Tamil Azerbaijani Sufedish (Swedish) Uzbek Albanian Fulani (Fula) Somaliyanci Rohingya Yarabanci (Yoruba)