Murnar cin kofin Championships League din PSG yasa mutane 2 sun mùtù dan sanda daya na can rai kwakwai mutu kwakwai a birnin Paris na kasar Faransa, an yi kòne-kòne da sace-sace
Rahotanni daga birnin Paris na kasar Faransa na cewa an yi kone'kone da sace sace da lalata dukiya a yayin da ake murnar cin kofin Championships League da kungiyar PSG ta yi.
Rahotannin sun kuma ce an kashe mutane 2 yayin murnar sannan an kama sama da 500 da suka aikata laifuka.
https://twitter.com/Megatron_ron/status/1928945703352410317?t=2ftRc57m_y3NgxI415Ud6g&s=19
Hakanan rahoton yace dansanda daya na can rai kwakwai mutu kwakwai saboda lamarin.
https://twitter.com/MegaGeopolitics/status/1929118696674361514?t=aMRoiiBdqoj7G4li9UZaXQ&s=19
'Yansanda sun fito da barkonon tsohuwa dan magance wannan matsala ta hatsaniya data kaure.








